Boko Haram sun kashe mutane a Attagara

Asalin hoton,
Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutane masu yawa, a wasu hare-haren da suka kai wasu kauyuka a jihar Borno.
A kudancin Borno ne 'yan kungiyar ta Boko Haram suka sace 'yan mata 'yan makaranta fiye da 200 a watan Aprilun da ya wuce.
Mazauna Kauyen Attagara dab da kan iyaka da Kamaru sun ce wasu mutane sanye da kakin soji, sun shiga kauyen zuwa harabar wani Coci kuma suka bude wuta.
Peter Biye, wani dan majalisa da ya fito daga yankin ya ce an kashe mutane an kuma kone gidaje da dama, a wasu kauyuka biyar da basu da nisa da Attagara.







