Chibok: Masu bore sun gana da jami'an tsaro

Asalin hoton, AFP
Gungun kungiyoyin da ke fafutukar ganin an ceto 'yan matan Chibok sun mika kokensu ga babban hafsan tsaron Nigeria, Alex Badeh.
Daruruwan mata da mazan sun bukaci dakarun tsaron kasar su dinga bayar da bayanin irin kokarin da suke yi game da ceton 'yan matan na Chibok.
Haka kuma sun bukaci jami'an tsaro su dauki matakan kare sace yara a jihohin da ke arewa-maso gabashin kasar da sauran gurare.
Sama da mako guda kenan daruruwan mata da maza ke yin jerin zanga-zanga da zaman durshen a sassa daban-daban na kasar.






