Gwamnonin arewa za su yi taro a Nigeria

Asalin hoton, Getty
A Najeriya, kungiyar gwamnonin arewacin kasar za ta gudanar da wani taron gaggawa a Abuja.
Matsalar tsaro da ake fuskanta a wasu jihohi na arewacin kasar da kuma babban taron kasa da ake gudanarwa a halin yanzu na daga cikin batutuwan da gwamnonin za su tattauna akai.
Haka kuma kungiyar za ta saurari jawabi daga tawagar gwamnonin arewacin kasar 13 da suka halarci wani taro da aka yi a Amurka tsakaninsu da wakilan gwamnatin Amurka da Denmark da kuma Norway kan yadda za'a magance matsalar tsaro da ake fuskanta a yankin.
Yayin da hukumomin tsaro a Najeriya ke cewa ana samun cigaba a yakin da ake yi da 'yan kungiyar Boko Haram, wasu na bayyana rashin gamsuwarsu da irin matakan da ake dauka a jihohi ukun da aka kafa dokar ta baci.






