An yi jana'izar mutane 106 a garin Izge

An yi jana'izar mutanan da aka kashe bayan harin da aka kai a garin Izge da ke karamar hukumar Gwoza ta jahar Bornon Nigeria.
Tsofaffi maza da mata ne ke aikin gina manyan kaburrukan da ake zuba gawarwakin, ganin babu sauran matasan da suka rage a garin.
'Yan Boko Haram ne ake zargin sun kai harin a daren Asabar inda suka kashe mutane kusan 106.
Majalisar Dattawa daga jihar Borno, Sanata Muhammed Ali Ndume ya ce 'yan bindigar sun shafe kusan sa'o'i biyar suna aika-aika ba tare da jami'an tsaro sun kawo dauki ba.
'Kaura'

Asalin hoton, AFP
Sakamakon harin da aka kai a garin na Izge, dubban mutane sun tsere zuwa karamar hukumar Madagali dake jihar Adamawa mai makwab taka don neman mafaka.
Hakan na zuwa kasada mako guda bayan da 'yan Boko Haram su ka yi kwantar bauna a garin Madagali suka kashe sojoji tara.
A makon daya gabata ne aka kai hari a garin Konduga na jihar Borno idan wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kashe mutane kusan 40 tare da kona daruruwan gidaje.
Da dama na ganin cewar dokar ta baci da shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya kafa a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe ba ya tasiri wajen magance matsalar tsaro a yankin arewa maso gabashin Nigeria.
Hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta ce kawo yanzu mutane 40,000 ne su ka gujewa rikicin Boko Haram a Nigeria su ka tsallaka zuwa makwabciyar kasar Niger.











