Boko Haram: An kashe mutane 106 a Izge

Asalin hoton, AFP
Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne a Najeriya sun kashe mutane sama da 100 a garin Izge na jihar Borno.
An yi janaizar fiye da mutum 60 da aka kashe a harin na ranar asabar da daddare.
Wadanda suka tsira a harin sun ce maharan sun tara mutane kamar 30 kana suka bude masu wuta
Daga bisani kuma suka yi ta bi gida-gida suna harbe mutane, yayin da suka yi wa wasu da dama yankan rago.
Yanzu haka dai dubban mazauna garin ne suka tsere zuwa Karamar Hukumar Madagali ta Jihar Adamawa.







