Kakakin majalisar dokokin Kano ya yi murabus

Wasu dai na ganin saukar tasa ba ta rasa nasaba da yiwuwar tsige shi

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto, Wasu dai na ganin saukar tasa ba ta rasa nasaba da yiwuwar tsige shi

Kakakin Majalisar dokokin Kano, Alhaji Garba Sallau, ya sauka daga mukaminsa.

Alhaji Sallau ya bayyana cewa ya ajiye mukamin ne saboda dalilai na siyasa.

Ya kara da cewa ba zai bar jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ba.

Wasu dai na gani saukar da kakakin majalisar dokokin ya yi na da nasaba da rade radin da ake yi cewa za a tsige shi daga mukamin.

A ranar Litinin ne dai 'yan majalisar dokokin jihar 26 cikin 32 suka fice daga jam'iyyar ta PDP zuwa jam'iyyar APC.

A karshen shekarar da ta gabata gwamnan jihar, Rabi'u Kwankwaso, da wasu gwamnoni hudu suka fice daga PDP zuwa APC, suna masu cewa jam'iyyar ta PDP ba ta da adalci.