Muna da mutane a jam'iyyar APC —Kwankwaso

Yayin da ake ci gaba da cece kuce dangane da rikicin da ya kunno kai a jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya, daya daga cikin gwamnonin da suka ta da kayar baya ya yi karin bayani kan halin da ake ciki gabanin taron da jiga-jigan jam'iyyar za su yi a ranar Talata mai zuwa.
Gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa suna cikin jam'iyyar ta PDP amma idan har aka kasa daidaitawa, suna da zabi dabam-dabam ciki kuwa har da shiga wata jam'iyyar.
Yace " idan shugabannin sun yi hattara za a sasanta, idan muka ga akwai matsala muna ta tsari, bamu da matsalar mu shiga APC saboda duk jiga-jiganta namu ne".
A ranar Alhamis ne dai gwamnan ya yi taro da dukkan masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP a Kano, inda suka tattauna kan halin da ake ciki.
Gwamnan Kwankwaso ya ce baya ga gwamnoni bakwai da suke cikin sabuwar PDP, akwai wasu gwamnonin da dama wadanda ba su bayyana kansu ba a fili, amma kuma sona goyon matakin boren da aka yi wa shugabancin Alhaji Bamanga Tukur.







