Mutane 15 sun kone a Lagos

Mutane goma sha biyar sun mutu sakamakon faduwar wata babbar motar daukar mai wacce ta kama da wuta a jihar Legas dake kudancin Nigeria.
Hadarin ya auku ne a kan babban titin Apapa zuwa Oshodi dake birnin a cikin daren ranar Talata.
Lamarin ya janyo konewar gidaje hudu, da motocin safa hudu da kuma shaguna 60 kafin a samu damar kashe gobarar.
Kakakin hukumar agaji ta kasar a Lagos wato NEMA, Ibrahim Farinloye ya tabbatar da afkuwar lamarin amma bai bayyana adadin wadanda suka samu raunuka sakamakon gobarar.







