An sace turawa a gabar tekun Nigeria

'Yan fashi a cikin teku sun kaiwa hari a wani jirgin dakon danyen mai a gabar tekun Nigeria, inda suka sace matukin jirgin da wasu injiniyoyi.
Jirgin mai suna MT ALTHEA na da mutane 18 a cikinsa lokacin da 'yan fashi su 10 su ka kai hari, su ka sace turawa biyu amma ba su taba man ba.
Rundunar tsaron ruwa a Nigeria ta ce tana binciken lamarin.
Sata a cikin tekun gabar yammacin Afrika ta karu da kashi daya cikin uku a wannan shekarar.






