Kotu ta daure Kabiru Sokoto rai da rai

Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yanke wa, Kabiru Sokoto daurin rai da rai a kurkuku saboda laifin kitsa harin bam ranar kirismeti a shekarar 2011 a arewacin Nigeria.
Lamarin ya janyo mutuwar mutane 44 lokacin da bam ya tashi a cocin St. Theresa dake Madalla a jihar Naija kusa da Abuja babban birnin kasar.
Kotun kuma ta samu Kabiru Sokoto da laifin shirya kai harin bam a shalkwatar 'yan sanda dake jihar Sokoto.
Sannan kuma ana zarginsa da horar da kusan mutane 500 wajen harhada abubuwan fashewa.
A ranar 14 ga Janairu 'yan sanda a Abuja suka damke Kabiru Sokoto amma bayan kwanaki biyu sai ya arce kafin daga bisani a gano shi a jihar Taraba.






