Ban shiga APC ba —gwamnan Niger

Gwamnan jihar Niger da ke Nigeria, Mu'azu Babangida Aliyu, ya musanta cewa yana cikin gwamnonin sabuwar PDPn da suka hade da jami'iyyar APC.
Don haka a cewar gwamnan ''ina nan a cikin jam'iyyar PDP''.
Kakakin gwamnan, Danladi Ndayebo, ya ce sun yi matukar kaduwa da jin labarin cewa gwamnonin sabuwar PDP sun hade da jam'iyyar APC ganin cewa ba a daddale kan batun ba.
Ndayebo ya kara da cewa gwamnan na Niger ba ya wajen taron da 'yan sabuwar PDP suka hade da APC.
A baya dai kafofin watsa labarai na Nigeria sun ba da rahotannin da ke cewa gwamnan na Niger ya janye daga cikin 'yan sabuwar PDP, sai dai gwamnan ya musanta zargin.






