Gwamnonin sabuwar PDP sun hade da APC

A Nigeria, 'yan sabuwar PDP karkashin jagorancin Alhaji Kawu Baraje da gwamnonin nan bakwai da suka balle daga jam'iyar PDP mai mulkn Nigeria sun hade da babbar jami'yyar adawar kasar, watau APC.
A taron da suka gudanar dazu a Abuja, bangarorin biyu sun amince su kalubalanci jam'iyar PDP a zaben shekarar 2015.
Gwamnonin da suka balle dai su ne gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, gwamnan Rivers, Rotimi Amechi, gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, gwamnan Jigawa, Sule Lamido, gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed, da gwamnan Niger, Muazu Babangida Aliyu.
Wannan hadewa da bangarorin biyu suka yi dai yana nufin yanzu haka suna da gwamnoni 18 a cikin 36 na Nigeria.
Sai dai kakakin gwamnan Niger, Danladi Ndayebo, ya ce har yanzu gwamnan jihar yana cikin jam'iyyar PDP.







