Najeriya ta yi na'am da ayyana Boko Haram 'yan ta'adda

Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi na'am da matakin da Amurka ta dauka na saka kungiyar Boko Haram da ta Ansaru a matsayin kungiyoyim 'yan ta'adda na kasashen ketare.
A wata sanarwa da ta fitar da yammacin ranar jumu'a, gwamnatin Najeriyar ta ce saka kungiyoyin cikin 'yan ta'adda na kasashen ketare zai kara yaukaka hadin guiwa tsakanin ta da Amurka wajen yaki da ta'addanci.
Haka kuma Najeriyar ta ce hakan zai kara karafafa yunkuri da amfani da doka wajen daukar kwararan matakai kan kungiyoyin biyu, zai kuma sa kasashen biyu su kara hobbasa wajen murkushe kungiyoyin 'yan ta'adda.
Gwamnatin Najeriyar ta kuma ce tana mai baiwa 'yan Kasar tabbacin cewa za ta bi duk hanyoyin da zata bi wajen shawo kan matsalar hare-haren ta'addanci, tare da kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
A kwanaki ukun da suka gabata ne ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bada sanarwar, inda ta ce matakin shine kadai hanyar da gwamnatin Najeriyar za ta bi wajen murkushe ayyukan 'yan kungiyar.






