Gobara ta tashi a kasuwar katako ta Jos

Gobarar da ta tashi a Lagos a watan Okotoba
Bayanan hoto, Gobarar da ta tashi a Lagos a watan Okotoba

Kayayyakin musamman hatsi da abincin dabbobi na miliyoyin naira sun salwanta, sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar Katako-Laranto dake Jos na jihar Filato.

Rahotanni sun nuna cewar gobarar ta tashi ne a cikin daren ranar Talata, kuma kawo yanzu babu bayanai game da hasarar rayuka.

Mutane da dama wadanda suka yi kokarin kashe wutar sun suma, sakamakon shakar hayaki a kasuwar.

Kasuwar Katako-Laranto na cikin manyan kasuwanni a birnin Jos, kuma ta sha fuskantar matsalar gobara.