Niger na tsoron samun Polio daga Nigeria

Mahukunta a Nijar na gudanar da rigakafin cutar polio ko shan inna a yankunan da ke kusa da Najeriya saboda gudun kar cutar ta tsallako iyakar kasar.
A bana dai ba'a sama rahoton ko da yara daya tak da ya kamu da cutar polio a jamhuriyar Nijar ba.
Sai dai a Najeriya da ke makwabtaka da kasar an sami yara fiye da 40 da suka kamu da cutar a bana.
Haka kuma ana yawan samun shige da fice tsakanin kasashen biyu.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce ana samun cutar Polio a kasashen Nigeria, Pakistan, Afghanistan da Syria ne kurum bayan da aka ci nasarar kawar da ita daga sauran kasashen duniya.






