Majalisa na duba hana Qatar jigila a Kano

Kwamitin Majalisar wakilai da ke kula da harkokin jiragen sama a Najeriya, zai binciki dalilin da ya sa aka hana kamfanin Qatar Airways, jigila a filin jirage na Malam Aminu da ke Kano.
Wasu 'yan majalisar na zargin cewa ma'aikatar da ke kule da harkokin jiragen saman kasar na nuna bangaranci wajen bai wa kamfanonin jiragen sama izinin jigila a wasu sassan kasar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar ta nuna damuwa game da wasu motoci da biyu masu sulke da aka saya wa Ministar harkokin sufurin jiragen sama, Misis Stella Oduah a kan sama da naira miliyon dari biyu.
'Yan majalisar sun bayyana cewa babu wani tanadin da aka yi a kasafin kudin ma'aikatar don sayen wadannan motoci, kuma wannan ya sa majalisar umurtar kwamitinta da ke kula da harkokin jiragen sama da ya binciki lamarin.






