Amnesty ta koka da kisan dalibai a Yobe

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta koka da yadda 'yan bindiga a arewacin Najeriya ke kai hare-hare kan dalibai da malamai.
'Yan bindigar sun hallaka daruruwan mutane tare da tilastawa dubunnai kauracewa makarantu a shekarun baya bayan nan.
A sabon rahoton da ta fitar, Amnesty ta ce hare-haren na kara tsananta, tare da nuna halin ko in kula ga hakkin gudanar da rayuwa da kuma na neman ilimi.
A harin baya bayan nan na ranar Lahadi, 'yan bindigar sun kashe kimanin dalibai hamsin ne a wata makarantar aikin gona da ke jihar Yobe.






