Rasha da China sun ce a yi taka tsan-tsan

Shugaba Xi Jinping da Shugaba Vladmir Putin
Bayanan hoto, Shugaba Xi Jinping da Shugaba Vladmir Putin

Rasha da China sun kara yin gargadi game da yinkurin amfani da matakin soji a kan Syria.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha ya ce kokarin wuce kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don kirkirar wata hujjar amfani da karfi a kan Syria, abu ne da zai janyo babban bala'i.

Moscow kuma ta soki matakin Amurka na dage tattaunawarsu a kan batun tashin hankalin.

Kamfannin dillancin labarai na gwamnatin China, Xinhua ya ce kasashen yammacin duniya sun yi gaggawar yanke hukunci a kan wanda ya yi amfani da makamai masu guda a Syria, tun kafin masu sa'ido na majalisar dinkin duniya su kamalla bincikensu.

A ranar Litinin Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya yi kalamai masu karfi a kan zargin kai hari na makamai masu guba a Syria, inda yace za a hukunta duk wanda aka kama da laifi.