Syria ta bar masu binciken makamai su yi aiki

Syria ta amince ta kyale masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya su ziyarci wani yankin dake wajen Birnin Damascus, inda ake zargin an kai hari da makamai masu guba a makon jiya.
Majaliar Dinkin duniyar ta ce jami'an nata zasu fara aiki a wurin gobe Litinin.
Majalisar dinkin duniyar ta ce gwamnatin ta amince zata dakatar da kai hare hare a yankin, a lokacin ziyarar jami'an a wurin.
Sai dai wani jami'in gwamnatin Amurka na cewa matakin da gwamnatin Syriar ta dauka a yanzu ya makaro, kuma gwamnatin Amurkar ta yi amannar cewa kusan babu wata tantama ita ce ta kai hari da makamai masu guba a kanfararen hula.
Ita dai gwamnati ta musanta wannan zargi.







