An kashe mutane 11 a Najeriya - 'Yan sanda

'Yan sanda a arewa maso gabashin Najeriya sun ce an kashe mutane goma sha daya a harin da aka kai gidan wani dan siyasa dake yankin.
Wani mai magana da yawun 'yan sandan jihar Adamawa, Mohammed Ibrahim ya ce an yi wa a kalla mutane biyu daga cikinsu yankan-rago.
Wadanda suka shaida lamarin a Kauyen Mildu sun ce mutanen da suka kai harin sun rinka kiran mutanen da suka kashe da sunayen su.
Ba a dai san wadanda suka kai harin ba a gidan Mataimakin gwamnan jihar ta Adamawa.
Dan siyasar dai ba ya gidansa a lokacin da aka kai harin.






