Adamawa/Pilato: an kai hare-hare

Taswirar Najeriya
Bayanan hoto, Taswirar Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa, an hallaka fiye da mutane goma sha biyar sakamakon wani hari da aka kai kauyen Midlu dake jihar Adamawa. A jihar Pilato kuma an kashe fie da mutane goma sha bakwai a yankin Wase.

A jihar Adamawa, an kashe mutane akalla goma sha ɗaya yayin da 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari a kauyen Midlu dake karamar hulumar Madagali.

An dai kai harin ne cikin daren jiya.

Yankin Wase dake jihar Pilato a arewacin Najeriya rahotanni na cewa, an kashe akalla mutane fiye da goma sha biyar yayin fadan ƙabilanci da aka soma tun daga daren jiya zuwa yau da rana.

Rahotanni na cewa, yanzu haka dai rikicin ya lafa, kuma 'yan sanda sun ce, tuni suka tura jami'an tsaro zuwa yankin.

Jihar Pilato dai ta shafe fiye da shekaru goma ana fama da rikicin dake da nasaba da kabilanci da addini, da kuma siyasa.