'Sojojin kasashen duniya za su fice daga Mali'

Ministan harkokin wajen Mali ya ce babu wata hujjar da za ta sa dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen duniya su ci gaba da zama a kasar idan aka ci galaba a yakin da ake yi da 'yan tawayen kasar.
Mista Tiéman Coulibaly ya kara da cewa ba yakin basasa ake yi a Mali ba, illa dai wasu bijirarrun mutane ne suka yi yunkurin tarwatsa kasar.
Tun da farko dai mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya shaidawa 'yan jaridu a birnin Paris cewa kasarsa ta amince da bukatar gaggauta kafa dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen duniya karkashin jagorancin kasashen Afrika a Mali.
A ranar Talata wakilan kasashen Turai da Afirka da Majalisar Dinkin Duniya za su yi taro a Brussels don tattaunawa a kan tsaro da kai kayan agaji, da kuma yadda za a kafa sabuwar gwamnatin dimokaradiyya a Mali.







