Dakarun Faransa sun kwace Timbuktu

Dakarun da ke yakar 'yan tawaye a Mali karkashin jagorancin Faransa, sun kwace iko da garin Timbuktu.
'Yan jarida a birnin sun ce dandazon jama'a sun yi maraba da dakarun Faransa da na Mali lokacin da suka shiga garin.
Ba a dai bayar da rahoton gwabza fada a wurin ba.
Shugaban Faransa Francois Hollande, ya ce dakarun na samun nasara kan 'yan tawayen.
Ana dai nuna damuwa kan dubban litattafai na tarihi da a ka ajiye a wani wurin adana tarihi, wanda aka tarwatsa kafin 'yan tawayen su fice daga garin.






