Masarautar Kano ta goyi bayan hana achaba

Ado Bayero
Bayanan hoto, Sarkin Kano Dr Ado Bayero ya tafi London domin jinya bayan harin da aka kai masa

Majalisar masarautar Kano ta goyi bayan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na hana daukar mutane a kan babura.

"Mai martaba Sarki yana goyon bayan dukkan matakan da gwamnatin Kano ke dauka domin tabbatar da zaman lafiya a jiharmu," kamar yadda Wamban Kano Alhaji Abbas Sanusi ya shaida wa manema labarai.

Wamban Kano wanda shi ne babban dan majalisar Sarkin na Kano, Ya kara da cewa gwamnatin Kano ta basu tabbacin cewa za ta samar da hanyoyin da za ta tallafawa mutanen da za su shiga cikin kunci sakamakon hakan.

Gwamnatin jihar ta Kano ta hana daukar mutane a kan babura ne bayan harin da aka kaiwa Sarkin na Kano Alhaji Ado Bayero a ranar Asabar.

An kashe direban Sarkin da kuma dogaransa biyu, sannan aka jikkata 'ya'yansa biyu a harin, sai dai Sarkin ya tsira.

Kungiyoyin masu sana'ar achaba da wasu mutane sun nuna damuwar cewa matakin zai jefa dubban jama'a cikin kunci da rashin aikin yi.

Sai dai hukumomi sun ce matakin ya zama wajibi ganin yadda ake amfani da baburan wurin aikata miyagun laifuka.