Soji sun cafke wani kusa a kungiyar Boko Haram

Rundunar Sojan Najeriya ta ce ta cafke daya daga cikin Shugabannin kungiyar nan ta Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.
Wata sanarwa ta ce an kame Mohammed Zangina ne a birnin Maiduguri.
Sojojin sun yi zargin cewa ya taimaka wajen shirya hare-haren kunar bakin-wake da dana bama-baman da a birane dabam-dabam na Najeriyar.
Rundunar tsaron hadin gwuiwa ta JTF a Maiduguri ta yi zargin cewa, Mohammed Zangina dan kwamitin Shura ne na kungiyar Boko Haram.
Mohammed Zangina na daga cikin mutanen da rundunar tsaron kasar ta ce tana nema ruwa a jallo, kuma ta sanya la'adar naira miliyan 25 ga duk wanda ya taimaka aka kamo su.






