Mataimakin Shugaban Masar ya yi murabus

Mahmoud Mekki
Bayanan hoto, Siyasar Masar na cikin rikici

Mataimakin shugaban kasar Masar, Mahmoud Mekki ya bayyana murabus dinsa yayin da Misiriwa ke ci gaba da kada kuri'arsu kashi na biyu kuma na karshe ta jin ra'ayoyin jama'a kan daftarin kundin tsarin mulkin da ya raba kan kasar.

Wata sanarwa da ta fito daga Mr Mekkin wadda aka karanta a gidan talabijin din kasar, ta ce dama tun wata guda da ya wuce ya ke san yin murabus amma bai yi ba sabili da abubuwan da suke faruwa, kamar harin da Isra'ila ta kai a Zirin Gaza.

A karkashin daftarin kundin tsarin mulkin za'a cire mukamin mataimakin shugaban kasa.

Masu sa ido na sa ran za'a samu mutane da dama da zasu amince da sabon kundin tsarin mulkin a kashi na biyu na kuri'ar jin ra'ayoyin jama'ar.