An yi bata kashi a birnin Iskandariya na Masar

An yi bata kashi tsakanin kungiyar 'yan uwa musulmi da kuma masu adawa da su, a gaban wani masallaci a birnin Iskandariya na Masar,kwana daya kafin a fara zaben raba gardama a karo na biyu a kan kudin tsarin mulkin kasar.
Jami'an tsaro sun harba barkonon tsohuwa domin raba bangarorin biyu.
Ko a makon daya gabata ma, saida aka samu tashin hankali a gaban wannan masallacin.
'Yan adawa a Masar dai na ganin gyaran da za'a yiwa kudin tsarin mulkin ya baiwa kungiyar 'yan uwa musulmi fifiko.







