Ana artabu tsakanin magoya baya da 'yan adawa a Masar

Magoya baya da masu hamayya da Shugaba Mohammaed Morsi na Masar na fada tare da bama baman da ake hadawa da fetur da kuma duwatsu a wajen fadar Shugaban kasa a Alkahira.
Dubbai kuma sun samu raunuka a yayinda 'yan sanda suka shiga tsakani domin kokarin dakatar da artabun, wanda ya soma a lokacin da magoya bayan Shugaban suka je domin tarwatsa wani sansanin 'yan adawa a wajen fadar Shugaban kasar suna zanga-zanga game da sabon daftarin tsarin mulki.
Shugabannin 'Yan adawa sun ce sun dora alhakin tashin hankalin a kan Shugaba Morsi.
Sun ce a shirye suke su sasanta idan ya soke wata dokar da ta ba shi cikakken iko sannan ya soke kuri'ar raba gardama da za a yi kan tsarin mulkin.






