Mai shigar da kara ya yi murabus a Masar

Talaat Ibrahim babban mai shigar da kara na Masar wanda ya yi murabus
Bayanan hoto, Talaat Ibrahim babban mai shigar da kara na Masar wanda ya yi murabus

Babban mai shigar da kara na kasar Masar Talaat Ibrahim ya mika takardar yin murabus bayan ya yi wata guda kacal a kan mukamin.

Shugaba Muhammad Morsi ne dai ya nada shi kan mukamin bayan karawa kansa iko a watan Nuwamba.

Murabus din ya biyo bayan zanga-zangar da jami'an bangaren shari'a suka yi inda suka bayyana sallamar tsohon mai shigar da karar kasar da Shugaban yayi ya nada wannan da cewa hari ne kan 'yancin da suke da shi.

Fiye da Alkalai da jami'an kotuna 1,300 ne su ka tattaru a wajen Ofishin Talaat Ibrahim ranar Litinin suna kira gare shi da ya sauka.

Sun kuma yi marhabin da labarin murabus din nasa da yin kirarin '' Allah ya ja zamanin shari'a !

''Muna shaidawa shugaban Jamhuriya, Mohammed Morsi, cewa Talaat Abdallah ya warware kashi casa'in cikin dari na wannan matsala ta hanyar matakin da ya dauka. Saura kai kuma ka warware sauran kashi goman ta hanyar mayar da Abdel Majeed Mahmoud kan mukaminsa.'' Inji Shugaban kungiyar Alkalai Ahmad Al-Zen.

Majalisar koli ta harkokin shara'ar kasar za ta yanke hukunci kan murabus din nasa wajen wani zama da zata yi ranar Lahadi.