'Yan adawar Ghana za su shigar da kara

Shugabannin babbar jam'iyar adawa ta NPP a Ghana sun ce suna duba yiwuwar shigar da kara a kotun kolin kasar, bayan da suka yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a makon jiya.
Hukumar zaben kasar dai ta bayyana shugaba mai ci wato John Mahama a matsayin wanda ya lashe zaben, to amma 'yan adawar sun ce an tafka magudi.







