Mai yiwuwa Jam'iyyar NPP a Ghana ta je kotu

Babbar jam'iyyar adawa a Ghana tace na duba yiwuwar shigar da ƙara kotu, domin a soke nasarar da Shugaba John Mahama ya yi a zaɓen shugaban Ƙasar da aka gudanar a ranakun juma'a da kuma asabar
Shugaban jam'iyyar NPP ya fadawa BBC cewar jam'iyyar za ta yanke shawara a ranar talata akan ko akwai isassun hujjoji dake tabbatar da cewar an tafka maguɗi a zaɓen.
Hukumar zaɓen ƙasar dai tace Mr Mahama ne ya lashe kashi hamsin da ɗigo bakwai cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa.
An yi taho-mugama tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan jam'iyyun adawa kafin bayyana sakamakon zaben.







