Yunkurin kawar da cin zarafin yara a intanet

An kaddamar da wani sabon yunkuri domin shawo kan cin zarafin yara a intanet.
Kasashe 48 ne za su shiga cikin gangamin, da suka hada da Australia, New Zealand, Najeriya da kuma wasu kasashen yankin Asia, Turai da Amurka.
Za a duba hanyoyin da za a rage wannan dabi'a da kuma kara yawan wadanda ake hukunta wa.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan kafin bude sabuwar cibiyar yaki da aikata laifuka a internet ta Turai a birnin Hague.
Sabon shirin yara kanana
Manufar dai na da aniyar shawo kan matsalar lalata da kananan yara a internet.
A bangare guda kuma, kamfanin Amazon na shirin kaddamar da wani shiri na musamman domin yara kanana.
Shirin wanda zai samar da fina-finai da litattafai da wakoki ba adadi daga dala 3 zuwa 10 a wata.
Za a fara kaddamar da shirin ne a Arewacin Amurka - da kuma manhaja a kwamfiyutar hannu ta Amazon Kindle Fire.










