Rashin aiki ya fi kamari a arewacin Najeriya

Rashin aikin yi yana daya daga cikin manyan matsaloli da suka yi wa Najeriya dabaibayi.
Masana dai sun yi ittifakin cewa rashin aikin yin da ke tafiya kafada da kafada da talauci, ya fi yawaita a tsakanin matasa da mata, musamman a arewacin kasar.
Sai dai hukumomin Najeriyar cewa suke yi suna bakin kokarinsu wajen samar da aikin yi don rage talauci a tsakanin matan da matasa.
A kwanan baya ne ma Hukumar samar da aikin yi ta kasar, NDE, ta kaddamar da shirin horar da mata kimanin 200 sana'ar tuka motocin kasuwa a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriyar, kafin kaiwa ga sauran jihohin, sana'ar da galibi maza ne suka fi mamayewa.






