Za a bude bankuna domin nakasassu a Najeriya

Asalin hoton, BBC World Service
A Najeriya, Babban Bankin Kasar wato Central Bank of Nigeria, ya ce bankuna a Kasar za su bude rassa na musamman domin nakasassu.
Hakan a cewar Babban bankin zai bai wa nakasassun damar gudanar da harkokin banki a saukake.
Hakan kuwa ya biyo bayan kiraye-kirayen da nakasassun su ka yi, don su samu kulawa ta musamman a Bankunan.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Malam Sanusi Lamido Sanusi ne ya zayyana hakan a wata ganawa da ya yi da shuwagabannin nakasassu na Najeriya.
Wannan na zuwa ne a lokacin da Kasar ke ci gaba da sauye-sauye a harkar bankunan don ci gaban Kasar.
Nakasassun dai a Najeriya sun yi maraba da wannan sanarwa ta babban banki






