'Sayen biredi a yanzu ya fi ƙarfina'

Asalin hoton, ASSOCIATION OF MASTER BAKERS AND CATERERS OF NIGER
Sakamakon ƙarin farashin kuɗin biredi, mutane da dama ba su iya cinsa saboda ba za su iya saya ba.
Mallam Ado Yahaya, tsohon ma'aikaci ne wanda ya yi ritaya kuma yana zaune a Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa ya daina amfani da biredi wurin karin kumallo tsawon lokaci sakamakon tashin farashinsa.
Malam Yahaya yana da yara tara, ya yi ritaya daga aikin gwamnati a 2020 kuma ya bayyana cewa idan yana so ya riƙa sayen biredi ga iyalansa sai ya kashe aƙalla naira dubu biyu a kowace rana yana mai cewa hakan zai sa ya kashe naira dubu 60 a duk wata.
"Shi ya sa ba mu iya cin biredi da safe sakamakon yadda ake yawan ƙara farashinsa, fanshon da nake karɓa ba zai isa na rinƙa sayen biredi ba a kullum, hakan ya sa na suaya zuwa abincin da nake da halin saya".
"Rabon da na ci biredi tun wani lokaci da na sayi wani ɗan ƙarami na ba yarana su tafi da shi makaranta," in ji shi.
Daga ranar Litinin, 27 ga watan Yunin 2022 ne ƙungiyar masu yin biredi ta sanar da cewa za ta ƙara farashin biredi da kashi 20 cikin 100.
Wannan na nufin za a riƙa sayar da babban biredi a kan 450 wanda a baya ake sayar da shi 400, haka kuma na 450 zai koma 500.
A cikin ƙananan biredi kuwa wanda ake sayarwa 130 zai koma 150. Haka shugaban ƙungiyar ta masu yin biredi reshen Jihar Ribas Chidi Orlu ya shaida wa BBC a yayin wata hira.

'Dalilin da ya sa farashin biredi ke yawan tashi'
Wannan ba shi ne karo na farko da masu biredi ke ƙarin kuɗi ba a cikin watannin baya bayan nan ba.
Orlu ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa ake ƙara farashin biredi shi ne ƙarin farashin kayayyakin haɗa biredi da ake yi kamar su biredi da fulawa da sikari da bota da yis da kuma ƙarancin wutar lantarki wanda da wutar ce ake sarrafa injinan yin biredin.
"Abin da ya ƙara ƙazanta lamarin shi ne ƙarin farashin dizal, sakamakon yanzu dizal ma ba a samun shi. Akasarin gidajen biredi a Fatakwal da Ribas na amfani da dizal ne," in ji shi.
Yadda yaƙin Rasha da Ukraine ya shafi farashin biredi
Yaƙin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine na taka rawa kan yaƙin Rasha da Ukraine.
Chidi Orlu ya bayyana cewa hakan ya faru ne sakamakon suna sayen sama da kashi 90 cikin 100 na kayayyakin da ake amfani da su wurin yin biredi daga Ukraine.
"Sama da kashi 90 cikin 100 na alkamar da muke amfani da ita muna shigo da ita ne daga ƙasashe kamar Ukraine, sakamakon yaƙin da aka fara, ba mu iya samun fulawar daga Ukraine, muna ƙoƙari domin ganin mun soma shigo da fulawa daga India.
"Amma kuma India na da jama'a da dama wanda hakan ya sa za a buƙaci sa hannun gwamnati domin sayarwa sauran ƙasashe kuma wannan zai iya kawo cikas.," in ji shi.
Mece ce mafita?
Kamar yadda Chidi Orlu ya bayyana, mafita ita ce gwamnati ta ƙara bayar da ƙwarin gwiwa wurin noman alkama, a ba manoman da suka dace iri mai kyau, da kayan aikin da suka dace da kuma shirin saka ido a kansu.
Ya bayyana cewa akwai buƙatar gwamnati ta bayar da tallafi ga waɗanda suka dace inda ya ce idan manoman cikin gida suka noma alkama za a samu raguwa a wadda ake shigowa da ita.
Ya kuma ce akwai buƙatar haɓaka noman rogo wanda za a iya amfani da shi wurin yin biredi. Haka kuma ya ce akwai buƙatar a rinƙa ba masu gidan biredi wani tallafi domin su ci gaba da gudanar da aikinsu sakamakon da dama daga cikinsu sun rufe wasu kuma ba su iya aiki kamar yadda suke yi a baya.











