Omar al-Bashir: Yadda 'yan Sudan suka fusata kan kalaman cin mutunci da aka ji lokacin sauraron karar tsohon shugaban kasar

- Marubuci, Daga Mohanad Hashim
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Wasu kalaman cin mutunci da nuna wariyar launin fata da aka yada kai-tsaye ta gidan talabijin na kasar Sudan lokacin wata gagarumar shari'a da ta shafi tsohon Shugaban kasar Omar al-Bashir sun haifar da fusata kan nuna wariyar launin fata da ke cigaba da mamaye al'ummar kasar Sudan shekaru uku bayan hambarar da gwamnatin shugaban da ya dade kan karagar mulki.
Gargadi: Wannan makala na kunshe da kalaman da mai yiwuwa wasu ba za su ji dadi ba
Tawagar lauyoyi masu bayar da kariya ga al-Bashir na tattaunawa a tsakaninsu a cikin zauren kotu a Khartoum babban birnin kasar, kuma ba su lura cewa na'urar daukar sautin magana na kunne ba.
An ji daya daga cikinsu na cewa: "Wannan bawan da wani mummunan hancinsa yana ba ni haushi."
Ana amfani da kalmar bawa da Larabci, "abd", wajen danganta mutanen da ake tunanin asalainsu 'yan Afirka ne a maimakon Larabawa - kuma kalma ce ta cin mutunci da ake amfani da ita wajen bayyana bakaken-fata.
Kalaman da aka yi a cikin sa'o'i uku da fara sauraron karar, ba su danganci sauraron karar da aka yada a gidan talabijin na kasar Sudan, da shafukan YouTube da Facebook na Kamfanin Dillancin Labarai na Sudan (SUNA) ba.
Mutanen na tattaunawa a kan wani fitaccen dan jarida ne Lukman Ahmed, wanda ba a dade da sallamarsa daga matsayinsa na daraktan kafar yada labaran kasar ba inda ni ma nake aiki.
Ahmed, wani tsohon wakilin sashen Larabci na BBC wanda dan asalin yankin Darfur ne, an nada shi a matsayin ne lokacin da gamayyar fararen-hula da sojoji ke mulki tare bayan hambarar da gwamnatin Bashir.
A watan Oktoba, janar-janar din sojin suka saba alkawarin mulkin gamayyar, suka kaddamar da juyin mulki.
Ahmed ya cigaba da kasancewa a kan mukaminsa na karin wasu watanni shida, amma daga bisani aka zarge shi da gazawa wajen mutunta shugaban mulkin sojin.
Wata muryar da aka nada ta lauyan ta karade ko ina, a yayin da da dama a shafukan sada zumunta suka yi saurin yin tur da kalaman nuna wariyar launin fatar game da Ahmed.
Hakan ya dawo da tunanin irin taken rikicin da ya faru a shekarar 2019 lokacin da masu zanga-zangar neman sauyi suka rika rerawa: "Ya ku masu girman kai da nuna wariyar launin fara, Darfur ita ce daukacin kasar.''

Asalin hoton, Getty Images
Ana yin wannan ne a kan Bashir, wanda ya fara mulki a shekarar 1989 a wani juyin mulkin da masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama suka mara wa baya, kana wanda ya kasance mai bakin jinni a kasashen duniya kan rikicin yankin Darfur.
Kotun Hukunta Masu Aita Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ICC ta tuhume shi da aikata laifukan yaki da kisan kare dangi a can, bayan da Larabawa mayaka masu rike da makamai da ake kira Janjaweed, a farkon shekarar 2000 suka fara kai farmaki kan kauyuka tare da fatattakar wadanda ba Larabawa ba - ko "Zurga", kalmar da ake dangantawa da al'ummomin bakaken fata.
Bashir ya ki halartar zaman kotun a Hague, kana ya musanta tuhumar da ake yi masa da cewa yarfen siyasa ne.
Ganin cewa lauyoyin Bashir ne suka furta wadannan kalamai, hakan ya sa masu neman sauyin na cewa Sudan ta dau hanyar komawa baya.
Duk da kasnacewar har yanzu Bashir da 'yan zamaninsa na cigaba da fuskantar shari'a, amma mutumin da ya mulki kasar Sudan na tsawon kusan shekaru 30, rike da mukamin soja mafi girma na field marshal, yanzu bay a gidan yari.
Tun bayan juyin mulkin ya kasance a wani asibitin sojoji mai zaman kan sa, kuma da dama sun yi amanna cewa daga karshe sojojin za su mayar da shi gida a karkashin daurin talala, a bisa dalilai na jin kai.
"Wannan sakamako ne na dabi'ar cin hanci da rashawa,'' shugaban Jam'iyar Sudanese Congress (SCP), wacce ke cikin hadakar fararen hular da aka yi wa juyin mulkin, ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Baya ga nuna fusata a shafin Twitter, Kungiyar Lauyoyi ta Darfur ta fito ta nuna goyon bayanta ga Ahmed, inda ta shigar da kara a madadinsa kan tawagar lauyoyin masu bayar da kariya da kuma lauyan.
Ahmed ya shaida wa BBC cewa an yi nufin "yaki da nuna wariyar launin fata, don kada ya bazu a cikin kasar ne".
Irin wannan nuna wariyar launin fata a kan ''babban bangare na kasar Sudan da kuma batun tausayawa a fadin duniya" a tsari na hukuma "daga mutane masu yin doka" abin takaici ne, in ji shi.
Karin munin abin, daya daga cikin lauyoyin ya kuma yi amfani da kalamai na sabo game da Ahmed, yana cewa ya la'anci addininsa - abin mamaki ya manta cewa shi ma dan jaridar Musulmi ne, a kasar da Musulmai suka fi rinjaye.
Tun bayan saun 'yancin cin gashin kai a shekarar 1956, halayyar nuna wariyar launin-fata ta zama ruwan dare a kasar Sudan, a bainar jama'a da kuma boye - na irin lokacin cinikin bayi na karni na 19 lokacin da Ottoman, 'yan kasuwar kasashen Turawa da Larabawa suka kaddamar da samame a kudanci don dawo da wadanda aka cafke a sayar da su.

Asalin hoton, AFP
Wani dadadden abu ne da aka yi Imani da shi cewa dabi'ar nuna wariyar launin fata daga manyan mutane a birnin Khartoum shi ne salsalar wannan gurbataccen abu a tarihin kasar.
Hakan ne ya ingiza 'yan Sudan ta Kudu neman 'yancin cin gashin kai da kuma rura wutar yin tawaye a kan nuna wariya a yankin Darfur, da tsunukan Nuba da kuma Blue Nile, wanda duka ke da ywan al'ummomin da ba Larabawa ba ne.
Nuna wariyar launin fata shi ne kuma abin da sauraron karar a kotun ta Hague ta mayar da hankali a kai, inda tsohon shugaban kungiyar mayakan 'yan tawayen Janjaweed ya musanta tuhumar da ake yi masa ta aikata laifuka kan bil adama a Darfur.
Ali Muhammad Ali Abd-al-Rahman, da har ila yau ake kira Ali Kushayb, shi ne mutumin farko da aka yi wa shari'a a kotun ta (ICC) kan rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 300,000 tare da haddasa wa mutane fiye da miliyan biyu rasa matsugunai.
Tun bayan juyin mulkin watan Oktoba, muhawarori a tsakanin jama'a sun kasance cike da kalaman nuna wariyar launin fata, da kalaman nuna kiyayya da kuma ingiza yin tashin hankali.
Darfur ta sake shaida tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci, kana aikata miyagun laifuka sun kara mamaye babban birnin kasar da sauran birane a cikin watannin baya.
Ana zargin kungiyoyi daga wajen birnin Khartoum daga kabilu daban-daban kan ayyukan dabar kan titina, wanda galibi kan kunshi masu rike da makamai a kan Babura da aka fi sani da "long nines" saboda yawan fasinjojin da ke hawa kai.
Shafukan sada zumunta cike suke da faya-fayen bidiyon 'yan banga na lakada wa 'yan daba duka, wanda ya kara rura wutar rikicin kabilanci.
'Yan dabar sun kasance masu alaka da 'yan tawaye daga kungiyoyi a yankuna kamar su Blue Nile, da Darfur da kuma tsaunukan Nuba, da suke ganin gwamnatin hadakar sun mayar da su saniyar ware, kuma tuni suka koma bayan sojoji - wanda a baya suke fada da su.
Mataimakin shugaban kasar Sudan Laftanal Janar Mohammed Hamdan ''Hemti'' Dagolo, na amfani da duka wadannan don muradunsa.
Fitattun mutane na yi masa kallon bako daga yankin Darfur, ya jagoranci babbar rundunar jami'an tsaro ta Rapid Support Force wacce ta samo asali daga kungiyar Janjaweed.
Amma wannan sabon kawancu da tsofaffin abokan gabarsa - sojojin hayar 'yan tawayen Darfur - sun kyale shi ya tafiyar mulkinsa.
Baya ga wannan gurabatacciyar hadaka shi ne cewa, yanzu Sudan ba ta da wata doka da ta yi wani tanadi wa aikata laifin nuna wariyar launin fata - da hakan ke nufin akwai yiwuwar Ahmed ba zai samu galaba a shari'arsa ba.
Duk da hakan, shi da magoya bayansa na da burin ganin cewa shari'ar za ta yi nuni da nuna wariyar launin fata ke cigaba da yin zagon kasa ka harkokin zamantakewa - inda daga bisani zai kawo sauyi.











