Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Ten Hag, Lukaku, Nunez, Hazard, Haaland, Lingard

Asalin hoton, EPA
RB Leipzig na shirin yi wa Manchester United yankan baya kan zawarcin mai horad da kungiyar Ajax Erik ten Hag na zama sabon kociyanta. (Telegraph - subscription required)
Paris St-Germain na tattaunawa da Chelsea domin sayen Romelu Lukaku shekara daya kacal bayan da kungiyar ta Premier ta sayo shi fam miliyan 98 daga Inter Milan. (But via Sun)
Manchester United da Arsenal sun bi layin kungiyoyin da ke zawarcin Darwin Nunez bayan da suka aika masu nema musu 'yan wasa su yi nazari a kan dan wasan na gaba dan Uruguay mai shekara 22 a wasan Benfica, a karshen mako. (Mirror)
Dan wasan Borussia Dortmund Erling Haaland,ya yi fatali da bukatarsa da Manchester United ke yi saboda dan kasar ta Norway yana ganin tsarin wasan kungiyar bai dace da burinsa ba. (ESPN)
Roma da AC Milan da kuma Juventus sun bi layin West Ham da Newcastle wajen bayyana bukatarsu ta daukan Jesse Lingard, mai shekara 29, idan kwantiragin dan wasan na Ingila ya kare da Manchester United a bazaran nan. (Mirror)

Asalin hoton, Getty Images
Ana ganin Borussia Dortmund na gaban kungiyoyi irin su Arsenal da AC Milan a nasarar zawarcin Eden Hazard, mai shekara 31, daga Real Madrid. (Cadena Ser - in Spanish)
Roma na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Aston Villa, Douglas Luiz, dan Brazil mai shekara 23, a bazaran nan. (Calciomercato - in Italian)
Manchester United na shirin yin garambawul a tsakiyarta a bazaran nan, inda ake sa ran Paul Pogba ya bar kungiyar idan kwantiraginsa ya kare a watan Yuni. (Mirror)
Ga alama ba lalle ba ne Tottenham ta samu damar sayen dan bayan Croatia Josko Gvardiol a bazaran nan, saboda matashin dan wasan mai shekara 20 yana jin dadin zamansa a RB Leipzig. (RB Live - in German)
Chelsea ta tuntubi dan wasan gaba nacibiyar horad da matasan 'yan wasan Arsenal Khayon Edwards kan bukatar daukansa a bazara, saboda har yanzu matashin dan Ingila mai shekara 18 bai kulla wata yarjejeniya ta kwararrun 'yan wasa da Gunners ba. (Goal)

Asalin hoton, Rex Features
Ana sa ran kungiyoyin Premier da sauran na Turai da dama za su gabatar da bukatarsu ta sayen dan bayan Chelsea Levi Colwill, a bazaran nan bayan da matashin dan Ingila mai shekara 19 ya nuna hazaka a zaman aron da yake yi a Huddersfield a kakar nan. (Fabrizio Romano)
Ana sa ran Marco Asensio zai bar Real Madrid a bazaran nan, inda AC Milan da Tottenham ke sha'awar dan wasan gaban na Sifaniya mai shekara 26. (Mundo Deportivo - in Spanish)











