Zamantakewa: Sirrin mallakar mijinki da na mallakar matarka

Bayanan bidiyo, Zamantakewa: Sirrukan mallakar mijinki da na mallakar matarka

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na 35 ɗin, shirin ya yi duba ne a kan sirrukan mallakar mijinki da na mallakar matarka.

Idan ke mace ce na san babban burinki bai wuce ki mallaki mijinki a tafin hannunki ba, haka kai ma namijin ba ka da burin da ya wuce a ce kai ne sitiyarin juya matarka yadda kake so.

To shirin zamantakewa na wannan makon zai ba ku sirrin mallakar miji da na mata ba boka ba mallam kuma ba tare da amfani da karfi ko cin zali ba.

Kyautata zamantakewar aure shi ya fi komai muhimmanci a zaman duniya, shi ya sa a wannan makon muka kawo muku ƙwararru don ba ku satar amsa.

Hajiya Aisha Ahly wacce ta rubuta littafi takanas bayan tattaro bayanai daga maza da mata ta gano me suka fi so idan ana son mallakarsu, ta wallafa sakamakon bincikenta a littafinta mai taken Sirrin Kwanciyar Hankali (Mijinki a Jakarki/Matarka a aljihunka.)

To a matsayinka na namiji, ta yaya za ka mallake matarka ka samu biyayyarta cikin ruwan sanyi?

Hajiya Aisha Ahly ta ce hanyoyi ne sauƙaƙa.

"Da yawa a kasar Hausa maza sun fi amfani da ƙarfi a kan mataynesu. Amma namiji mai hikima wanda kuma yake samun kwanciyar hankali, shi ne mai sassauƙan hali, mai kyakkyawan fata, mai kuma ƙoƙarin kyautata wa iyalinsa, mai ƙarfin hali, mai dauriya, mai ba da uzuri.

Ta ƙara fda cewa idan namiji na son saka matarsa a aljihunsa, to dole ya kyautata mu'amalarsa da ita, sirrin kwanciyar hankalinka na cikin kyautatawarka da saukakawarka.

"Ka dinga yi wa matarka fara'a da yi mata kyauta da yabawa hankalinta, ka girmamata, ka kula da ita, ka sauke hakkokinta da Allah Ya dora maka, aannan ka zama mai yawan kyautatawa," in ji Hajia Aisha.

Hakkun kyautatawa ba irin biyayyar da ba za ta sayo maka ba, balle ma dai a ce ka ƙara da kyautatawa iyayenta da ƴan uwanta da duk wanda ya rabe ta, sululuf za ka cusa ta a aljihu ka juya ta son ranka.

Wannan layi ne

Wasu na baya da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

'Ba boka ba malam'

Shi ma Sheikh Muhd Auwal, wani malami da ya fi yin nazari kan zamantakewar al.'umma, ya bai wa maza matakan mallakar mace.

Ya ce na farko dole namiji ya ji tsoron Allah a kula da iyalinsa, ya girmamata da kyautata mata, ya kuma zama mai ba ta lokacinsa.

Ya kuma kamata maza su san cewa ba a tursasawa da saka tsauri wajen mallakar soyayyarta, amma ana iya mallakarta ta hanyar kyautatawa da mutuntawa.

To ke kuma 'yar uwa me za ki yi don mallakar miji ba boka ba malam?

Hajiya Aisha ta ce wannan sassaukar hanya ce ga wace ta sani kuma take son bi, "shi namiji babu abin da ya fi buƙata fiye da biyayya da ladabi.

"Sannan ki zama mai iya kwallaiya, da tsafta da iya girki da kula da dukiyarsa da 'ya'yansa, sannan ki iya hira don an ce hira ma iyawa ce," a cewarta.

'Yar uwa anan fa iya hira aka ce ba wai zuba surutu ba, kar ki je ko miskilin miji gare ki ki hau surutu ba waƙafi ba aya ba har sai kin ƙular da shi.

Sannan ki sani ba a sa wa namiji karfi wajen mallakar soyayyarsa, amma ana iya mallaka ta hanyar kyautatawa da biyayya.

Abu na karshe shi ne, a duk lokacin da mata da miji suke kan turbar aure, manyan abubuwan da suke bukata daga wajen juna, su ne yarda da amincewa, sai kuma su yi ta hakuri da juna tare da zama jarumai a kan al'amuran junansu.

Wannan layi ne