Zamantakewa: Shin mata kulawa suka fi so fiye da kuɗi?

Bayanan bidiyo, Zamantakewa: Shin mata kulawa suka fi so fiye da kuɗi?

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na 25 din, shirin ya yi duba ne kan me mace ta fi so a zamantakewa, kudi ko kulawa?

Mutane da dama suna dauka cewa mace ta fi son kudi fiye da komai a tattare da namiji, musamman a zamantakewar rayuwa.

Anya haka abin yake? Shirin zamantakewa na wannan makon batun da zai duba kenan.

Da a ce kudi mace ta fi so fiye da komai, ciki kuwa har da kulawa, na tabbata da aurarrakin manyan masu kudin duniya ba su mutu ba.

Amma a nan baya-bayan nan a kan idanuwanmu auren mutumin da ya fi kowa a kudi a duniya, wato Jeff Bezos ya mutu, ba mu gama farfadowa daga kaduwar hakan ba, sai ga shi mai bi masa a arziki Bill Gates shi ma sun rabu da matarsa. Kai da ma dai wasu misalan da ke faruwa a kewayenmu.

Tirkashi, to idan da tsantsar arziki ke rike maka mace a gida, ai da wadancan hamshakan ba za a taba yarda a rabu da su ba.

Kar ku ce don dai su Turawa ne. Mata a duk inda suke, in ban da bambancin addinai da al'adu, kusan a halayya dai sukan yi tarayya, da baturiya da balarabiya da bahaushiya da ma kowace kabila ce.

Mata da dama da na dade ina tattara ra'ayoyinsu duk sun ce min sun fi bukatar kulawa da riritawa fiye da komai.

To ko yaya maza suke kallon lamarin?

Husnah Kamshi ta ce daga cikin irin rashin kulawar da mace ta fi tsana a nuna mata sun haɗa da a dinga nuna mata rashin kula ta fannin auratayya da nuna ko in kula da al'amuranta da kuma Rashin nuna yaba mata a lokutan da ta yi wani abin ƙwarai.

Shi ma Nasiru Na'ammani Gwarzo ya haƙiƙance cewa mata sun fi son kulawa fiye da komai, don haka yake shawartar maza ƴan uwansa da su bi wannan layi.

Maza kar ku bari dai a garin kallon ruwa kwado ya yi muku ƙafa, idan budurwa ce da kai nuna mata so da ƙauna da kulawa ka ga yadda za ka samu shiga.

Idan matarka ce, nuna mata so da ƙauna da kulawa ka ga zallar sadaukarwa.

Idan kwalliya ta yi, yi ta zuga ta kana yabonta, kai baby kin ganki kuwa, kamar wata zahra don haske.

Idan abinci ta yi, ka ce kai tawan, wannan girki kamar a birnin Sin.

Idan ba ta da lafiya, yi ta tarairayarta da lallashi. Ka san Allah da wadannan, za ka mallake ta tsaf babu musu ba gardama

Amma kar ku sha'afa kudin ma muna so a dinga ba mu, duka cikin lallashi da nuna kulawar ne.