Zamantakewa: Rayuwar mace da zamantakewarta a al'umma
Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashi na 33 ɗin, shirin ya yi duba ne a kan illaharin zamantakewar mace a cikin al'umma.
Mace, halitta mai daraja wadda rayuwar zamantakewarta ke cike da kalubale da kuma tarin albarkoki.
Shirin zamantakewa na wannan makon ya yi duba ne a kan illaharin zamantakewar mace a cikin al'umma, abin da ake mata na rashin dadi da ita ma wanda take yi na rashin kyautawa, sai kuma mu duba tarin alkhairorinta.
Bari mu duba irin matsalolin da mace kan ci karo da su a zamantakewa kafin mu je ga alkhairan.
Rayuwar mace gaskiya akwai fannin wahala da na sauki amma ta ce fannin wahalar ya fi yawa.
Ta zayyano manyan wahalhalu biyar da mata suka fi cin karo da su a wannan zamanin., tun daga shekarun kuruciyarta zuwa na girmanta.
Sannan ga matsin lamba idan ba ta samu yin auren da wuri ba a saka ta a gaba kamar ita ta hana kanta.
Balle kuma idan aka ce ta hadu da kaddarar mutuwar aure ko ta miji, a nan ma ba karamin bone mata ke shiga ba musamman idan aka ki kyautata zamantakewa da su a lokacin.
Ba a ma labarin daukar ciki da renonsa da azabar nakuda da fadi tashin reno da tarbiyyar 'ya'ya
Sannan a wasu lokuta ne ma za a ga idan ɗa ya lalace sai a dinga danganta laifin a kan uwar, idan kuma ya zama nagari sai a nuna kamar babu kokarinta a ciki.
Duk da wannan kokari kuma ba ta tsira ba a wajen wasu, sai ka ji ana mace karamar kwakwalwa gare ta ko tunaninta ragagge ne.
Malama Zahra'u ta ce "na san mata da yawa da suka mutu sanadin wahalhalun zamani, mace a bar a tausaya mata ce.
Kar ma dai idan aka zo batun kan wadanda ke haduwa da kaddararren aure.
Mace ce fa wacce idan ta yi sa'ar aure da sa'ar miji sai al'umma su bi ta da zargin mallake shi ta yi, idan ta yi aure ba ta samu haihuwa da wuri ba sai a dora lafin a kanta a tsame mijin.
Idan kuma ƴaƴa mata take ta haifa sai a ce duk ta cika masa gida da mata ba ɗa namiji, idan ƴaƴa maza Allah yake ta ba ta kuma sai a ce oho ka bari tana ta mallake ma gida da haihuwar maza.
Abubuwa dai barkatai ga su nan.
Wasu na baya da za ku so ku gani
To amma bari mu zo kan albarkoki da alkhairorin mace mana
Malama Zahra'u ta ce sannan kuma mata na cikin kangin jin dadi musamman idan ta yi sa'ar miji na gari.
Ita ce wacce aka sanya aljannar ƴaƴa a karkashin kafarta. Aka kuma ce a wajenta ne namiji ke samun nutsuwa.
Malama Zahra'u ta kuma aannan kuma rayuwa ta nai mata dadi idan 'ya'ya sun girma sun zama na gari ababen alfahari.
Baya ga haka kuma mace ce wacce Ubangijinta yai mata gatan sanya mata mai tsaronta, mai kula da ita kuma mai jibintar lamarinta a kowane mataki na rayuwarta.
A lokacin kuruciyarta da tasowarta aka sanya mahaifinta a matsayin wakilkinta, a shekarun aure aka dora nauyinta a kan mijinta, a shekarun girma lokacin ko da ba mijin sai aka ce danta ya zama mai kula da al'amuranta.
Ta ko ina dai zagaye take da masu tsaro masu kula kamar yadda dokar kasa take baibaye shugaban kasa da masu tsaronsa.
Ita ce abar kaunar mahaifinta, a bar son mijinta, abar girmamawar kannenta maza, a bar kulawar yayyenta maza, a bar mutuntawar ƴaƴanta maza, sannan sanyin idaniyar jikokinta.
Kan batun tunaninta da kwakwalwarta kuma, idan dai aka ba ta ilimi na addini da na zamani, to ta kan zamewa iyalanta babbar special adviser saboda tsabar tsinkayenta.
Jan hankali
Sadiq Gwarzo ya jawo hankalin yan uwa maza kan kyautata wa mata da daina zarginsu a kan wasu abubuwan musamman kula da hakkin mata.
Mace wacce a cikin gida bayan mijinta ya zama Chief executive, ita kuma ta zama ministar harkokin ciin gida, minsitar kasafi da tsare-tsare, sannan babbar ministar harkokin abinci da tabbatar da tsaftar muhalli.
A karshe don jin dadin zamantakewarki, ke ma ya kamata ki kiyaye da kula da wasu abubuwan.
A inda kika tsinci kanki a zaman kishi, to ki zama mai adalci da rage gaba da mugunta, a inda kika zama uwar miji to ki zama mai nagarta da rike surukarki cikin adalci, a idan kika zama matar ɗa, to ki kyautata da yi wa uwar mijinki ladabi. Ai ko ba komai ciwon 'ya mace na 'ya mace ne.
Sannan a karshe ki zama marufar asirin mijinki, mai kyautata zamanki da shi da yin biyayya cikin abin da ubangiji ya yi umarni sannan ki kyautata mi'amalarki da kowa ma d zama ya hadu.












