Zamantakewa: Miji da matar da ya kamata matasa su duba don aure
Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashi na 32 ɗin, shirin ya yi duba ne kan mijin da matar da ya kamata matasa su duba don aure.
Husband material, wife material, su ne kalmomin da suka fi fitowa daga bakin matasa a wannan zamanin idan suna maganar burukansu na aure.
To wai idan ka ji budurwa ko saurayi suna ta babbatun fatan samun husband material ko wife material, me suke nufi da hakan ne?
Bari mu shiga cikin shirin zamantakewa na yau inda za mu ji abin da matasan ke nufi da husband and wife material.
Na ji yo ta bakin wassu da dama ta bayan fage matan kan fassara husband material ne da hadadde, wanda ya gama kafuwa ya kama ƙasa, mai babban aiki a hannu, mai yan canji, mai gida da mota ko ma gidaje da motoci, a takaice dai namijin novel kamar yadda wasu ke cewa.
Su kuma samarin da yawansu da na dan bibiyi yadda suke ganin abin ta baya fage
Sai a ji suna fassara wife material da hadaddiya, doguwa, fara, kyakkyawa ta aje wa a gaban mota, wani ma ji za ka yi ya ce fara ko mayya ce.
A wannan gaɓa ce muka ga dacewar a matsayinmu na iyayensu kuma yayyensu gara mu gaya musu gaskiya tun kafin duniya ta gaya musu.
To wai wane irin abokin zama ko abokiyar zama ya kamata matasan su dinga fata da rububin samu don wanzar da zamantakewa mai kyau da kafa iyali na gari?
Shirin ya tattauana da Hajiya Fatima Chikaire, wata uwa a Abuja da kuma Dr Ibrahim Rijiyar Lemo wani babban malamin addinin Musulunci a Kano.
Wasu na baya da za ku so ku gani
Duk da dai ba duka aka taru aka zama daya ba, daga cikin matasan akwai masu ra'ayi dabam da na wadancan, wadanda su bil hakki idan suka ce husband ko wife material suna nufin wadanda idan ma aure ne ya kullu to za su zauna lafiya da juna.
Dama masu magana kan ce ta yaro kyau take ba ta ƙarko, a wannan karon muna fatan Allah Ya sa ta yi kyan kuma ta yi ƙarkon.
Da fatan matasa sun ji waɗannan shawarwari na neman abokan zama na gari.
Idan namiji ne yana da kyau ya duba mace mai hankali da nutsuwa da ilimin addini da ma na zamanin inda hali, mai kunya, kuma mai yakana, 'yar gidan mutunci, a iya barin kyau daga karshe idan dai har an sami wadannan na farkon.
Idan mace ce kuma gara ki duba mai hankali mai ilimin addini da na zamani shi ma inda hali mai nutsuwa mai yakana mai hangen nesa.
Sannan mai rufin asiri wanda yake da hanyoyin halal na ciyar da ke da tufatar da ke da ba ki muhalli da kula da sauran bukatunki kuma dan gidan mutunci, don ba auren mai kudi ne kawai jin dadin aure ba.












