‘Yan ci-ranin Afirka da kasar Italiya ke zargi da fataucin mutane

A cikin jerin wasikunmu daga 'yan jaridar kasashen Afirka, Ismail Einashe ya hadu da wani matashi dan kasar Senegal wanda aka zarga da yin fataucin mutane jim kadan bayan da ya tsira daga nutsewa a Tekun Bahar Rum.

Mai shekaru 16 daga kasar Senegal, ya tsira inda ya tsaya a tsibirin Sicily - yana kuma zaune a inda ake kira cibiyar ajiye 'yan ci-rani.

Wannan a shekarar 2015 ne bayan da ya tsallake rijiya da baya a wani bulaguro mai cike da hadari daga kasar Libya. Amma bayan kwanaki biyu a wurin ya shiga damuwa cewa kofar dakin da yake ciki a kulle take.

Babu zato babu tsammani, kawai sai Moussa - wanda aka sauya sunansa saboda boye ko shi wane ne - ya samu kansa cikin gidan yari a Trapani, wani birni mai tashar jiragen ruwa na kasar Italiya.

"Wannan ba mai yiwuwa ba ne, na shiga kasar Italiya kuma kai-tsaye na shiga cikin gidan yari. Shekaruna 16," ya rika tunani a ransa.

Ya kasa amincewa da abin da ya faru da shi, wanna ba kasar Turai da yake da burin zuwa ba ce kafin ya fara bulaguron mai cike da hadari daga kasar Senegal don neman rayuwa mai kyau.

Moussa zai shafe kusan shekaru biyu a gidan yarin da ake kulle manya, kan tuhumarsa da ake yi da fataucin mutane duk da cewa shi mai kananan shekaru ne.

Lamarinsa ya fita da ban ne.

A cikin shekaru goma da suka gabata, mutane fiye da 2,500 ne aka cafke a kasar Italiya kan irin wannan tuhuma, kamar yadda wani sabon rahoton kungiyar Arci Porco Rosso mai zaman kan ta da ke da mazauni a birnin Palermo.

An zargi wadanda aka cafke a kasar ta Iyaliya da taimakawa da kuma da kuma aikata laifin safarar 'yan cirani, laifin da sakamkonsa shi ne zaman gidan kaso na shekaru 20 da kuma tara mai yawan gaske.

'Dora musu laifin wasu'

Yanzu haka akwai daruruwan 'yan ci-ranin da ba su ji ba ba su gani ba da aka garkame suna jiran a kammala tsare-tsaren yi musu shari'a, kamar yadda Maria Giulia Fava, wata lauya wacce ta taimaka wajen rubuta rahoton ta bayyana.

Ta bayyana cewa kasar Italiya na amfani da dokokin masu fataucin mutane wajen mayar da 'yan gudun hijira da 'yan cirani a matsayin masu aikata laifi, a wani yunkuri na dora musu laifin wasu a matakai na kaurar jama'a.

Akan tuhumi 'yan ci-rani kan shaidun da ba su taka-kara sun karya ba, ta kara bayyanawa, ba a cika bude sauraron kararraki a kotu ba, kana akwai rashin wadatattun damar samun kariyar shari'a, ana amfani da shaidun da ba a tabbatar da su ba, kana masu kananan shekaru kan kare a gidan yarin da manya suke.

Cheikh Sene ya san yadda tsarin gidan yarin yake.

Yanzu shi ne jami'in tsare-tsare na kungiyar al'ummar kasar Senegal a Palermo babban birnin tsibirin Sicily, amma ya shafe shekaru biyu a gidan yari bayan da aka same shi da aikata laifin taimakawa wajen safarar mutane, kuma bayyana cewa 'yan cirani da dama ana kulle su a gidan yari ba bisa adalci ba, don kawai sun ceci rayukan jama'a a cikin teku.

Ya bayyana cewa abinda ya faru da shi kenan.

Kungiyar Arci Porco Rosso ita ma ta bayyana a rahotonsu cewa sun ci karo da irin wadannan abubuwa inda jami'an 'yansandan Italiya also state in their report that they suka bai wa 'yan cirani takardun izini a madadin bayar da shaidar zur a kan matuka jiragen ruwa da ake zargi.

Ma'aikatar Shari'a ta kasar Italiya ta shaida wa BBC cewa ba za ta iya samar da bayanai game da shari'oi da cafke cafken mutane ba, amma ta bayar da bayanai kan wadanda a ake tsare da su a gidan yari a yanzu, kan tuhumar safarar mutane.

Daga ranar 22 ga watan Maris, ta ce, akwai fursunoni 952 inmates, da 562 daga cikinsu aka yanke musu hukunci a Italiya kan fataucin.

Amma kuma, ma'aikatar ba ta ce komai game da zarge-zargen da aka yi a cikin rahoton kungiyar Arci Porco Rosso ba.

'Kananan yara a cikin kurkukun manya'

A game da abinda ya faru da Moussa lokacin da jirgin ruwansa ya sa birnin Trapani, an bar sa shi ya sauka kana ya jira tare da sauran wadanda suka isa a tsashar jiragen ruwan don jiran motar safa din da za ta dauke su zuwa cikin gari.

Amma a yayin da yake zaman jira a can wasu jami'an kasar Italiya suka kira shi.

"Sun bukaci da in bi su ciki. Sun ba ni wasu takardu, kana suka dauki hotona.

"Daga nan suka sa na shiga cikin wata babbar mota kana suka tuka suka tafi da ni. Mun shafe fiye da sa'oi biyu muna tafiya, kana suka kai ni cikin ofishinsu.''

Ofishin 'yansanda ne inda aka rika yi masa tambayoyi da hanyar wata tafinta 'yar kasar Morocco mai jin harshen Faransanci.

Ta yi masa bayani cewa wasu fasinjoji biyu sun zarge shi da tuka jirgin ruwan.

Ya roke su don su fada masa ko su wanene wadannan mutane biyu, saboda ya kasa gane zargin da ake yi masa, amma ta fada masa cewa ita tafinta ce ba lauya ba.

Da gari ya waye aka saka shi a cikin motar 'yan-sanda.

"Ban san cewa gidan kukuku za a kai nib a, Na yi tsammani wurin ajiye 'yan ci-rani ne.''

Ya yi kokarin bayyana musu cewa shi karamin yaro ne. A cikin kukukun, ya bayyana cewa an yi masa binciken kwakwaf don gano shekarunsa. Wani binciken ya gano cewa shi karamin yaro ne, a yayin da wani yan una akasin haka.

Saboda sakamakon bai kammala ba aka saka shi cikin kukukun manya.

Kana ya ce ba shi kadai bane a cikin wannan yanayi. Ya tuna da sauran matasan 'yan ci-ranin Afirka masu shekaru irin na sgi da wadanda bas u kai shi ba a cikin kukuku tare da shi.

Ya tuno da haduwa da 'yan kasar Gambia, da Tunisia, da Najeriya da Mali da dama.

Mahaifinsa ya rasu ba ya nan

Watanni tara kafin ya iya kiran 'yanuwansa a kasar Senegal da suke tsammani yam utu.

Bayan watanni kadan, a kiran waya na biyu ya gano cewa mahaifinsa ya rasu.

A kurkukun ya samu akalla ya yi karatunsa na sakandaren Italiya kana ya far tunanin tserewa daga gidan yarin.

Daga karshe, a shekarar 2017, Moussa ya samu ranar sauraron kararsa a kotu da ke birnin Palermo.

Amma a lokacin da ya shiga zauren kotun, alkalin ya tashi tsaye y ace ba zai jagoranci zaman kotun a kan karar da aka shigar kan karamin yaro ba.

Daga nan, bayan kwanaki uku da sanyin safiya jami'an tsao suka zo cikin dakin da aka kulle shi kana suka bukaci ya tattara kayansa saboda an sallame shi.

"Sun raka ni zuwa bakin kofa, kana suka rufe kofar daga bayana. Ina tsaye a can, da ledar zuba shara cike da tufafi na.''

Ba san inda zai dos aba, kana daya daga cikin masu gadin suka ba shi shawarar taka zuwa bakin hanya har sai ya hadu da sauran 'yan kasar Afirka ya tambaye su shawara kan abinda ya kamaya ya yi.

A wannan daren a dandalin Piazza Vittoria a birnin Trapani. A can ya hadu da wasu 'yan kasar Senegal da suka fada masa da ya nufi Volpita, wani sansanin 'yan cirani.

Daga karshe Moussa ya bar sansanin Volpita bayan jin cewa zai iya samun kudi ta hanyar tsinkar 'yayan zaitun a wasu wurare.

Bayan shafe watanni da dama yana aiki a can ya koma da zama a wani sanannen gari na 'yan yawon bude ido da ake kira Cefalù, kusa da birnin Palermo, inda yanzu yake aiki a matsayin mai dafa abinci a wani otal.

Amma har yanzu ba a yi komai game da abinda ya same shi ba, kuma har yanzu yana cikin wani yanayi na damuwa game da zaman rashin sanin tabbas.

Tardunsa zamansa sun kare kuma yana jiran sabon kwanan watan komawa zaman kotu.

A yayin da Moussa ke bayyana irin halin da ya shiga na shekaru shida bayan zuwansa kasar Italiya ya kasance cikin damuwa - dimuwa kan halin da ya shiga. Yana kawai bukatar ganin wannna abin tsoron ya kawo karshe.