MDD za ta binciki mutum 142 kan zargin aikata muggan laifuka a Sudan ta Kudu

.

Asalin hoton, AFP

Ƙwararru a Majalisar Ɗinkin Duniya sun fitar da sunayen mutum 142 da za a gudanar da bincike a kansu kan take haƙƙin bil adama a Sudan ta Kudu.

Laifukan da ake zarginsu da aikatawa sun haɗa da kisan kiyashi da azabtarwa da garkuwa da mutane da sata da ƙona ƙauyuka da tilasta wa mutane barin muhallansu da fyaɗe kamar yadda hukumar kare hakkin bil-Adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya reshen Sudan ta Kudu ta tabbatar.

Yasmin Sooka wadda shugabar hukumar ce a reshen Sudan ta Kudu, ita ta gabatar da waɗannan zarge-zargen a wani rahotonta ga hukumar a Geneva.

Ta ce duka mutanen da aka rubuta sunansu, sun cancanci a gudanar da bincike a kansu kan laifuka da suka aikata na cikin gida da na ƙasa da ƙasa, ciki har da rawar da suka taka wajen rura wutar rikicin siyasa.

Yaƙin basasa ya ɓarke a 2013 bayan Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar sun yi hannun riga, lamarin da ya yi sanadin mugun rikici da aka yi ƙiyasin mutum miliyan huɗu sun rasa muhallansu.

Mutanen biyu sun yi gwamnatin haɗin gwiwa a 2020 amma wannan bai dakatar da rikicin siyasa da na ƙabilanci ba.

Ms Sooka ta bayyana cewa laifukan da hukumarta ke bincike sun nuna ƙarara yadda ƴan boko ke gwagwarmayar neman mulki ƙarfi da yaji.

Ba a fito fili an bayyana sunayen waɗanda za a bincika ba - amma Ms Sooka a baya ta ce akwai mutane daga duka ɓangarorin biyu waɗanda ake zargi da aikata laifukan.

Ta ce rashin ɗaukar hukunci mai tsauri na daga cikin abubuwan da suka jawo matsalolin da Sudan taa Kudu ke fuskanta kuma ga shi ana shirin gudanar da zaɓe a shekara mai zuwa.

Har yanzu gwamnati ba ta ce komai ba dangane da kalamanta.