Buhari ya gana da Mai Mala kuma ya yarda ya ci gaba da shugabancin APC

Asalin hoton, Faruk Aliyu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci kungiyar gwamnonin APC mai mulkin Najeriya ta bar gwamnan Jihar Yobe kuma shugaban rikon jam'iyyar, Mai Mala Buni, ya ci gaba da shugabancin jam'iyyar.
Ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aike wa shugaban gwamnonin jam'iyyar APC, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi. Hakan na faruwa ne a yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Mai Mala Buni a birnin Landan ranar Talata.
Buhari ya ce ya fahimci rigimar da ke faruwa a cikin jam'iyyar lamarin da ya sa aka kai kara kotu, yana mai cewa duk da haka ya amince Mai Mala Buni ya ci gaba da jagorancin babban taron jam'iyyar da ake shirin gudanarwa a ranar 26 ga watan Maris, duk da wani umarnin kotu da ya ce a dakatar da taron.
Kazalika a wata wasika da shugaban kasar ya aike wa shugaban gwamnonin jam'iyyar APC, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, Shugaba Buhari ya bukaci a guje wa abubuwan da za su dagula jam'iyyar yana mai cewa "da farko batun shugabancin riko na jam'iyya zai komo kamar yadda yake a baya."
Hakan na faruwa ne a yayin da Jam'iyyar APC ta jaddada cewa Mai Mala Buni zai karɓi aikinsa da zarar ya koma gida daga tafiyar da ya yi.
Shugabancin APC ya shiga ruɗani ne a ƙarshen watan Fabarairu tun bayan da aka ga Gwamnan Neja Abubaukar Sani Bello ya fara jagorancin kwamatin. Daga baya kuma wata wasiƙa ta ɓulla cewa Mai Mala ne ya ba shi riƙo saboda ya yi tafiya ƙasar waje don a duba lafiyarsa.
Rikicin shugabanci a APC ya ƙara ƙamari ne tun bayan da wasu gwamnoni, ciki har da Nasir El-Rufai na Kaduna, suka ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin a sauke Mai Mala Buni, wanda ya fara jagoranci tun watan Yuni na 2020.
Lamarin na zuwa ne yayin da jam'iyyar ta fara shirin gudanar da babban taronta na ƙasa da za a yi ranar 26 ga watan Maris, inda za a zaɓi shugabanni a matakin ƙasa baki ɗaya duk da wani umarnin kotu da ya ce a dakatar da taron.
"Shirya sahihin taron ƙasa cikin nasara a ranar 26 ga watan Maris ne babban muradin kwamatin kuma za mu ci gaba da shirin yin hakan har zuwa lokacin da shugaba zai dawo kuma ya karɓi aikinsa," a cewar sanarwar da sakataren kwamatin ya fitar ranar Talata.
Tuni aka fara sayar da fom ɗin takara ga masu son yin takarar shugabancin jam'iyyar kan naira miliyan 20.
Shugabancin APC ya shiga ruɗani ne a ƙarshen watan Fabarairu tun bayan da aka ga Gwamnan Neja Abubaukar Sani Bello ya fara jagorancin kwamatin. Daga baya kuma wata wasiƙa ta ɓulla cewa Mai Mala ne ya ba shi riƙo saboda ya yi tafiya ƙasar waje don a duba lafiyarsa.
Sanawar da Sakataren Riƙo na Ƙasa John James Akpanudoedehe ya fitar ta sake jaddada cewa ba a sauke Mai Mala daga muƙamin ba da kuma sauran 'yan kwamatin kamar yadda wasu gwamnonin jam'iyyar suka bayyana a baya.
'Babu wani rikici a APC'
Rikicin shugabanci a APC ya ƙara ƙamari ne tun bayan da wasu gwamnoni, ciki har da Nasir El-Rufai na Kaduna, suka ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin a sauke Mai Mala Buni, wanda ya fara jagoranci tun watan Yuni na 2020.
Sanarwar ta Mista Akpanudoedehe ta ce babu wata ɓaraka a jam'iyyar tasu, yana mai cewa "kanmu a haɗe yake wajen samar wa ƙasa shugabanci na gari".
Ya ƙara da cewa sun kafa wani kwamati da zai lalubo musu hanyoyin kauce wa umarnin kotun da ya dakatar da gudanar da taron.
'Gwamnoni ba su da ra'ayi sai abin da Buhari ya ce - Gwamnan Jigawa
Gwamnan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ya ce shi da sauran gwamnonin da ke mara wa Shugaba Muhammadu Buhari baya ba su da ra'ayin kansu sai abin da shugaban ya amince da shi.
Ya bayyana haka ne a tattaunwa ta musamman da BBC Hausa.
Gwamnan ya ce ba shi da wani ra'ayi kan inda mulki zai koma a shekarar 2023, yana mai cewa a matsayinsa na shugaban kwamitin na jam'iyyarsu bai kamata ya bayyana ra'ayinsa ba.












