Abin da Buhari ya ce kan rudanin jagorancin jam'iyyar APC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi gargaɗi ga ƴaƴan Jam'iyyar APC kan rikicin shugabanci da ya dabaibaiye jam'iyyar mai mulki.
A cikin bayananin da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Buhari ya yi kira ga ƴan jam'iyyarsa da su gujewa koƙarin tayar da zaune tsaye a APC kafin babban taronta na ranar 26 ga watan Maris.
Saƙon na Buhari na zuwa ne yayin da ake jayayyar shugabancin APC na riƙon ƙwarya tsakanin ɓangaren gwamnan Yobe Mai Mala Buni da kuma ɓangaren gwamnan Neja Abubakar Sani Bello.
A cikin saƙonsa, Buhari wanda yake hutu a birnin Landan bai ambaci ɓangarorin biyu ba da kuma jayayyar da suke ta shugabancin riƙo na APC.
Sai dai shugaban ya alaƙanta da kamanta rikicin jam'iyyar hamayya ta PDP, yana mai cewa ya kamata ya zama darasi ga APC.
"Dole mu kalli PDP mai ƙarfi a baya da yanzu ta tarwatse, kuma mu koyi darasi da rashin haɗin kansu da rashin iya gudanar da mulki da kuma rashawa," in ji Buhari.
APC ta rabe gida biyu a wasu jihohi na Najeriya, Buhari ya ce rikicin jam'iyya ba sabon abu ba ne a sassan duniya. "Amma rabuwar jam'iyya saboda son rai ba zai haifar da ɗa mai ido ba ga makomar jam'iyyar," in ji shi.
Buhari ya kuma bayyana rikicin da abin da ya kira raba hankalin jam'iyyar gabanin babban taronta na zaɓen shugabanni. Ya ce haɗin kai ne zai zama tsanin ci gaba da samun nasarar jam'iyyar a dukkanin ɓangarori na Najeriya.
APC mai mulkin Najeriya ta faɗa sabon ruɗani ne bayan gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya yi iƙirarin karɓar jagorancin jam`iyyar a matsayin muƙaddashin shugaba na riƙo.
Daga baya kuma Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya fito ya ce har yanzu shi ne halastaccen shugaban riƙo na Jam'iyyar.
Rikicin jam'iyyar ana ganin ya raba kawunan ƴan jam'iyyar har ma gwamnonin da ke cikinta ana kyautata zaton kansu ba a haɗe yake ba.
Gwamnan Kaduna Nasir El Rufai ya yi iƙirarin cewa Shugaba Buhari ne ya ce Gwamnan Neja Abubakar Sani Bello ya karɓi jagorancin jam'iyyar a matsayin shugaban riƙo.
Hakan na nufin an tuɓe gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai mala Buni daga shugabancin jam'iyyar. Sai dai, wasu ƴan kwamitin riƙon jam'iyyar sun musanta hakan.
Jayayya shugabancin riƙo ta Gwamna Mai Mala da Gwamna Sani Bello ya yi a matsayin muƙaddashi, ya sa mutane da dama suna dasa ayar tambaya a kan lamarin, inda wasu ke cewa da alama salo ne na mamaya.
Haka kuma rashin samun bayanai daga fadar shugaban ƙasa kan iƙirarin da ake yi na Shugaba Buhari ne ya amince da sauke shugaban riƙon ko kuma kore batun ya ƙara dagula lamura.











