Har yanzu Mai Mala ne Shugaban APC na riƙo - Sanata Jajere

.

Har yanzu tsugune ba ta ƙare ba a Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ganin cewa Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya ce har yanzu shi ne halastaccen shugaban riƙo na Jam'iyyar kamar yadda wani jigo a jam'iyyar ya tabbatar wa BBC.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan Gwamna Nasir El Rufai ya yi iƙirarin cewa Shugaba Buhari ya ce Gwamnan Neja Abubakar Sani Bello ya karɓi jagorancin jam'iyyar a matsayin shugaban riƙo.

Sai dai bayan wannan ikirarin na El Rufai, wata wasiƙa ta rinƙa yawo a shafukan sada zumunta mai ɗauke da sa hannun Gwamna Mai Mala Buni wadda ta nuna cewa ya bar wa Gwamna Sani Bello riƙo ne kawai.

Sanata Alkali Abdulkadir Jajere wanda jigo ne a jam'iyyar APC kuma makusanci ga Gwamna Mai Mala, ya tabbatar wa BBC da sahihancin wannan wasiƙa inda ya ce sakamakon rashin lafiyar da Mai Mala Buni yake fama da shi ne ya rubuta wasiƙar domin ya je a duba lafiyarsa.

Ya bayyana cewa ya rubuta wannan wasiƙa ne domin kada ayyukan jam'iyya su tsaya ganin cewa an yi jadawali na babban taron jam'iyya.

"Abin mamaki shi ne cewa bayan da wannan wasiƙa ta isa hannunsu kuma suna sane da wannan wasiƙa kuma aka zo aka ce wai wani ya zo ya shiga shi ne shugaban riƙo," in ji shi.

Sanata Alƙali ya tabbatar wa BBC da cewa Mai Mala Buni na nan kan kujerarsa ta shugaban jam'iyya na riƙo inda ya ce Mai Mala da kansa ya tabbatar masa da cewa har yanzu shi ne shugaba.

Haka kuma Sanata Alƙali ya yi watsi da iƙirarin Gwamna Nasir El Rufai da ya yi a gidan talabijin na Channels inda ya ce El-Rufai ba kakakin Shugaba Buhari ba ne inda ya ce idan ma Shugaba Buhari ya faɗi haka za a ji ne ta bakin Malam Garba Shehu ko kuma Femi Adesina.

Rikicin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya dai na ci gaba da ɗaukar sabon salo inda ake ganin kawunan ƴan jam'iyyar ya rabu har ma gwamnonin da ke cikinta ana kyautata zaton kansu ba a haɗe yake ba.

Kuma duka waɗannan rikice-rikice ba su rasa nasaba da batun wanda za a tsayar takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2023 ƙarƙashin inuwar jam'iyyar.