Wahalhalu biyar da 'yan Najeriya ke ciki a wannan lokaci

Layukan mai

Masu lura da al'amuran yau da kullum na ganin ƴan Najeriya sun sake faɗawa cikin wata wahalar abubuwan more rayuwa da suka daɗe da mantawa da ita.

Wahalhalun na ƙaruwa a ƙasar daga wani ɓangare zuwa sauran ɓangarori, kamar yadda wasu ƴan ƙasar ke cewa "ana cikin wani yanayi a Najeriya"

Ko da yake hukumomi a ƙasar na nanata cewa suna ɗaukar matakai na shawo kan matsalolin da ke tagayyara ƴan Najeriya a lokacin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓen shekarar 2023.

Ga wasu wahalhalu biyar da ƴan Najeriya ke ciki:

Wahalar fetur

wahalar mai

Asalin hoton, Getty Images

An shafe makonni ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a jihohi da dama na Najeriya, lamarin da ya haddasa wahalhalu ga masu ababen hawa baya ga ƙaruwar farashin sufuri.

Najeriya ce kasar da ta fi kowace kasa samar da man fetur a nahiyar Afirka wadda kuma take samar da kusan ganga miliyan biyu ta ɗanyen mai.

Duk da arzikin mai da Allah ya ba ƙasar amma wahalar fetur ba sabon abu ba ne a Najeriya. Ko da yake an daɗe ba a shiga wahalar fetur ba a ƙasar.

Ƴan ƙasar sun shiga wahala ne tun lokacin da aka shigo da wani gurɓataccen mai ɗauke da wani adadin sinadarin methanol da ya zarce abin da ƙasar ta iyakance a kasuwa.

Ƴan ƙasar da dama sun yin kukan cewa man da suka saya a gidajen mai ya lalata musu abubuwan hawa. Daga baya hukumomin sun ce an magance matsalar.

Matsalar ta jefa ƴan Najeriya cikin wahala, inda ake samu dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai.

Wahalar mai na shafar ɓangarori da dama na buƙatun yau da kullum da ke dogaro da fetur, lamarin da ke ƙara haifar da wahala ga ƴan Najeriya a ɓangarori da dama.

Ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu wato IPMAN ta musanta cewa ɓoye man fetur da ake zargin wasu dillalai ke yi shi ne ya ƙara ta'azzara ƙarancin man fetur da ake yi a Najeriya.

Wata matsala da ta kunno kai a baya-bayan ita ce ta karancin man dizel, inda a yanzu haka farashin sa ya tashi zuwa naira 700 a kan kowace lita.

Yawanci manya da matsakaitan masana'antu da tsirarun gidaje duk sun dogara man dizel wajen gudanar da harkokin yau da kullum.

Harajin da gwamnatin kasar take samu daga kamfanonin man fetur da kuma kudaden da take samu na kasashen waje ta hanyar fitar da man yana taka muhimmiyar rawa ga tattalin arzikin kasar.

Sai dai wasu masu ruwa-da-tsaki akan man fetur sun ce matsalar tana da nasaba da tashin da farashin man fetur ya yi a kasuwannin duniya.

Masu ruwa-da-tsaki a kan harkar man fetur, sun danganta tashin da man dizel ya yi da tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya, sakamakon yakin da Rasha ke yi a Ukraine, da kuma cire tallafin mai da gwamnatin Najeriya ta yi.

Tsadar tikitin jirgin sama

Jirgin Sama

Asalin hoton, Other

Tsadar farashin tikitin jirgin sama na ɗaya daga cikin wahalar da ƴan Najeriya suka shiga.

Hauhawar farashin tikitin jirgin sama da kuma rashin tabbas sun jefa fasinjoji cikin halin damuwa da ƙaƙa-ni-ka-yi.

Tun a watan Fabrairu dukkanin jiragen Najeriya sun ƙara farashi inda suka mayar da ƙaramin tikiti zuwa na N50,000.

Jiragen sun ƙara kuɗi ne sakamakon ƙarancin man da jirgin sama ke amfani da shi, lamarin ke ci gaba da kawo tsaiko a harkokin sufurin jirgin sama.

Kamfanonin jiragen sama sun yi gargaɗin cewa matsalar na iya tilasta musu katse harkokin sufuri ta sama a ƙasar.

Baya ga tsadar farashin jiragen, matsalar ta kuma haifar da samun jinkiri ga fasinja da soke tashin wasu jirage.

Ƙarancin man jiragen ya haifar da tsadarsa a kasuwa inda wasu jiragen suka ce farashin ya tashi daga N590 zuwa N625 duk lita ɗaya.

A watan Fabrairun 2021 jiragen na sayen lita ne kan N190, amma zuwa ƙarshen shekarar farashin ya kai tsakanin N350 zuwa N370.

Ƙarancin kuɗaɗen ƙasashen waje da tsadar farashin mai a kasuwar duniya su suka haifar da tsadar farashin man jiragen.

Satar mutane don kuɗin fansa, na cikin dalilan da suka sa ɗumbin mutane suka gwammace hawa jirgin sama duk da tsadar tikitinsa.

Sai dai, ga alama duk da tsadar, a yanzu hawa jirgin sama ya fara zama, ga mai ƙaramin ƙarfi sai da wani babban dalili.

Tsadar farashin kayan masarufi

Kayan abinci

Asalin hoton, Getty Images

Duk lokacin da ake wahalar fetur da dizel, za a fuskanci tsadar farashin kayan masarufi da sufuri.

Ƴan Najeriya na fuskantar wahalar abubuwan wahalar mai da kuma tsadar kayayyaki.

A rahoton da ta fitar a watan Fabrairu hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta ce hauhawan farashin kayayyaki ya ƙaru da kashi 1.63 a Fabrairun 2022 wato ƙarin kashi 0.16 idan aka kwatanta da watan Janairu.

Ƙarancin lantarki

Wahalhalun

Asalin hoton, Getty Images

Al'ummar Najeriya na ci gaba da kokawa kan rashin wutar lantarki, wadda hakan ke kara haddasa matsin tattalin arziki.

Al'umma a sassan ƙasar na ci gaba gaba da rayuwa cikin zafi da duhu musamman da dare saboda ƙaruwar rashin wutar lantarki.

An daɗe ƴan Najeriya na fama da matsalar ƙarancin lantarki.

A baya-bayan nan ɗaukewar lantarki ya ƙaru inda rahotanni a ƙasar ke cewa katsewar babban layin raba wutar ya shafi jihohi da dama ciki har da Lagos da Enugu da Kaduna da Abia da Abuja da Anambra da Ebonyi da Enugu.

Ministan lantarki na Najeriya, Injiniya Abubakar Aliyu ya shaidawa BBC cewa masu fasa bututun mai ne suka taba na gas da injunan lantarkin ke amfani da su.

Ya ce suna duba wasu hanyoyi na yadda za a samar da lantarkin domin amfanin jama'a.

Rashin wadatacciyar wutar lantarki a Najeriya, abu ne da ke ci wa al'ummar kasar tuwo a kwarya musamman wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.

Duk da kasancewar Najeriya babbar kasa mai arzikin ma'adanin kwal da man fetur da iskar gas, sannan kuma wadda ta fi kowacce fitar da danyan fetur a nahiyar Afirka, rahotannin sun nuna kashi 40 cikin 100 na al'ummar kasar ne kadai ke samun wutar lantarki.

Rashin wutar lantarki dna janyo matsaloli da dama musamman wajen tafiyar da abubuwa da suka hada da kasuwanci da bangaren aikin gona da masana'antu da asibitoci da makarantu da sauransu.

Hakan yakan janyo mutuwar masana'antu da kuma dakile habbakar kananan sana'o'i.

Yajin aikin malaman Jami'a

Wakilan gwamnati da na ASUU

Asalin hoton, @fkeyamo

Yajin aikin da malaman Jami'an ke yi, wata matsala ce da ta jefa rayuwar ɗalibai cikin rashin tabbas.

Yajin aikin malaman kusan ya zama ruwan dare, wani mataki da suke ɗauka domin neman gwamnati ta biya buƙatunsu.

Sai dai ya fi shafar ɗalibai da kuma makomar karatunsu, wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.

A ranar litinin Kungiyar malaman jami'o'in ASUU, ta sanar da tsawaita wa'adin yajin aikin da suka tafi zuwa makwanni takwas sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnati kan bukatunsu.

ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami'a na kasar.

ASUU kusan ta shiga yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.