Hotunan da suka fi jan hankalin duniya da yin tasiri a 2021
Mawaƙiya kuma masaniyar tarihi Kelly Grovier ta ɗauki hotuna mafi ban mamaki a wannan shekara - ciki har da hotunan wata yarinya da ke duban ɗakin kwananta da aka jefa wa bam a Gaza da kuma tarzomar Capitol na Amurka - kuma ta kwatanta su da zane-zane masu ban mamaki.

Asalin hoton, Getty Images
Yaro mai kama da ƙarfe
Wani yaro ɗan shekara takwas yana bara a kan titunan Depok na kasar Indonesia. Fatarsa shafe da wani fentin ƙarfe mai guba da man girki wanda ya canza launin jikinsa bai-ɗaya kai ka ce wani sassaƙen mutum ne da aka cinna wa wuta ya babbake.
Aldi, na cikin gungun wasu mutanen da ake kira Manusia Silver a Indonesia, waɗanda ke daukar wa kansu irin wannan mummunan mataki don kawai su ja hankalin jama'a su ji tausayinsu, su taimaka musu.
Hoton Aldi a tsakiyar ababen hawa a kan titin birnin ya yi matuƙar tasiri.

Asalin hoton, Getty Images
Yarinya a Gaza, Mayu 2021
A wani rikici mafi muni da ya ɓarke tsakanin Isra'ila da Falasdinawa tun shekara ta 2014, hare-haren jiragen sama na baya-bayan nan da Isra'ila suka kai (a matsayin ramuwar gayya ga makamin roka daga Hamas) ya rusa gidansu wata karamar yarinya a Beit Hanoun, a Gaza a ranar 24 ga watan Mayu.
Hoton yarinyar da kuke gani a tsaye babu takalmi a cikin tarkacen gidan nasu tana kallon waje yana da taɓa zuciya.

Asalin hoton, Reuters
Jawabin ministan harkokin wajen Tuvalu a taron COP26
Ministan harkokin wajen Tuvalu Simon Kofe kenan lokacin da yake gabatar da jawabi ga taron tattauna matsalar sauyin yanayi a aka yi a Glasgow.
Wani abun jan hankali game da hoton shi ne yadda ministan ya gabatar da jawabinsa a cikin wani ruwa da ya taru, domin nuna yadda matsalar sauyin yanayin ke da matuƙar tasiri.
"Ba za mu taɓa zuba ido muna kallo ba" in ji Kofe, a daidai lokacin da ruwan ke tsiri a kusa da shi."

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan sama-jannati, Isra'ila 2021
Wasu ƴan sama-jannati biyu suna tafiya kafada-da-kafada a cikin rigar sararin samaniya yayin aikin horar da Mars a ramin Ramon Crater a hamadar Negev ta Isra'ila.
Wuri mafi yawan sahara a duniya, "makhtesh" na da matukar muhimmanci ga Isra'ila musamman ta fuskar bincike.
An yi amfani da wajen a matsayin duniyar Mars, domin horar da ƴan sama-jannatin.

Asalin hoton, Getty Images
Yar ninƙayar China a watan Janairun 2021
A watan Janairu, an dauki hoton wata mata tana ninƙaya daga wani dutsen kankara dake tasowa daga wani tafki mai sanyi a Shenyang, dake lardin Liaoning na arewa maso gabashin China.
Daskarewa sama da saman gilashin ruwa mai ɗaci, ta kasance har abada a dakatar da ita - ba wani lokaci ba ko a wajensa, mara nauyi ko nauyi.
Ga mutane da dama, yanayin wannan wasa ba abu ne mai sauƙi ba.

Asalin hoton, Getty Images
Rikicin Capitol, Amurka, Janairun 2021
Hotunan magoya bayan Donald Trump na yin artabu da 'yan sandan Capitol a ranar 6 ga watan Janairu, sun girgiza duniya.
Mutanen sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da tabbatar da Joe Biden a matsayin zababben shugaban kasa.

Asalin hoton, Environmental Photographer of the Year 2021
Yaro mai shaƙar Iska
A watan Nuwamba, an bayyana waɗanda suka yi nasara a gasar ɗaukar hotunan da suka shafi muhalli ta shekarar 2021.
A wannan rukuni ne hoton wani matashi da aka nuna yaro sanye da na'urar taimakawa wajen yin numfashi ya ciri tuta
An dauki hoton ne a Nairobi, Kenya, kuma ba wai kawai yana nuni bane da halin da ake ciki, face ita kanta makomarmu da ka iya cewa marar tabbas.
Hoton na kuma nuni da yadda tarihin fasaha yake a can baya.

Asalin hoton, Getty Images
Zane, Oktoba 2021
Hoton ma'aikatan kashe gobara na Faransa suna tayar da bargo mai hana wuta don kare wata dimbin dukiya a babbar cocin Saint-Andre a lokacin wani atisaye a Bordeaux a Faransa a watan Oktoba, shi kansa aikin fasaha ne.
Masanin Flemish na ƙarni na 17 Yakubu Jordaens ne ya ƙirƙiri zanen a tsakiyar hoton kuma yana kwatanta wani mutum mutumi da aka gicciye da dogayen sanduna sanye da soso a kan wani duhu mai kauri.
Durkokin da ke gefen zanen na da wasu wurare da ke kamanceceniya da tudu da gangare a lokaci guda.

Asalin hoton, Getty Images
Yara a Habasha, Hoto: Yuli 2021
A watan Yuli an dauki hoton wasu kananan yara a tsaye a karkashin bishiya a wani wuri da za a gina sansanin 'yan gudun hijirar Eritriya a nan gaba, kusa da kauyen Dabat da ke arewa maso gabashin birnin Gonder na kasar Habasha.
Wani zaren ganyan bishiyar da kwanto kansu ya ƙara wa hoton armashi.
Ya kasance wani misali na abubuwa da dama a tarihin al'adu da wasu bishiyoyi da aka taba yin yayinsu tun tale-tale.

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatan lafiya a Indiya, Oktoba 2021
Don murnar yi wa al'ummar Indiya biliyan guda riga kafin korona, wasu ma'aikatan jinya a Asibitin Ramaiah da ke Bangalore.
Sun fito a watan Oktoba don ɗaukar hoto, kowaccensu na riƙe da allura, wata alama ta abubuwan da suka yi amfani da su wajen samun wannan nasara.











