Muhimman abubuwa da suka faru a Najeriya a 2021

Asalin hoton, Nigerian Army
Shekarar 2021 ta zama mai ƙalubale a Najeriya, kamar sauran ƙasashen duniya, tun daga matsalar tsaro da tattalin arziki da hauhawan farashin kayyaki da kuma annobar korona ta ƙara dagula al'amura a ƙasar.
Sauya manyan hafsoshin tsaro
Shekarar 2021 ta fara da nasara ga sojojin saman Najeriya inda a ranar 1 ga watan Janairu suka kai wasu hare-hare ta sama a kan wani sabon sansanin Boko Haram da ke garin Mana Waji na jihar Borno. Dakarun sun samu nasarar kisan gwamman 'yan kungiyar.
Sai dai bayan mako biyu ƙungiyar ISWAP ta kai wani samame kan sansanin sojojin Najeriya a Marte, kuma ta ce ta kashe sojoji bakwai tare da kama ɗaya.
Kwana 10 da afkuwar haka, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke hafsoshin sojin kasar, inda Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya maye gurbin Lafatanar Janar Tukur Burutai a matsayin babban hafsan sojin Najeriya.
Sai dai a watan Mayu ne sabon babban Hafsan sojin ƙasa Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya rasu sakamakon hadarin jirgin saman soji a Kaduna. An kuma maye gurbinsa da Manjo janar Farouk Yahaya.
Saudiyya ta taso ƙeyar ƴan Najeriya

A watan na Janairu ne ƙasar Saudiyya ta taso ƙeyar ƴan Najeriya kusan 400 daga cikin fiye da 800 da ke tsare a gidajen yarin kasar.
An killace su kafin aka mayar da kowa jiharsa.
Rufe Masallacin Sheikh Abduljabbar

Labarin ya ja hankali a Najeriya musamman a arewacin ƙasar shi ne na rufe Masallacin Sheikh Abduljabbar da gwamnatin Kano ta yi bisa zargin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma tunzura al'umma, wani abu da ya sa shehun malamin da gwamnatin Ganduje yin musayar yawu.
Lamarin ya kai har aka gudanar da muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da wasu malamai a Jihar Kano ranar Asabar, 10 ga watan Yulin 2021 wadda gwamnatin jihar ta shirya.
Ranar Juma'a 16 ga watan Yuli ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama'a, zargin da ya sha musantawa.
Satar ɗaliban makaranta

An shiga tashin hankali a Najeriya a 2021 inda ƴan bindiga suka saci ɗaliban makarantar sakandare musamman mata
A ranar 24 ga watan na Fabrairu ne ƴan bindiga suka yi awon gaba da ƴan makarantar mata ta garin Jangebe da ke jihar Zamfara su fiye da 400, kafin daga baya aka kubutar da su.
Wannan na zuwa yayin da ake kokarin kuɓutar da daliban makarantar sakandiren Kagara da malamansu da yan bindiga suka sace a jihar Neja a ranar 17 ga watan Fabarairu.
A ranar 27 ga watan Fabrairu aka sako ɗaliban Kagara da malamansu da ma'aikata guda 41 da 'yan bindiga suka sace.
A watan Maris ne masu garkuwa suka yi awon gaba da 'yan makarantar koyon aikin gona da ke Mando Kaduna su 30.
A ranar 20 ga watan na Afrilu ne kuma 'yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai 20 da malamai 2 na jami'ar Greenfield University da ke Kaduna.
A ƙarshen watan na Mayu, wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da 'yan makarantar Islamiyya a garin Tagina da ke jihar Naija.
A ranar 26 ga watan Yuni jihar Kebbi ta fuskanci nau'in farko na satar 'yan makaranta, inda 'yan bindiga suka kutsa makarantar gwamnatin tarayya da ke Birnin Yauri suka yi garkuwa da ƴan mata fiye da 30, bayan kashe dan sanda guda sakamakon fafatawa da suka yi.
A farkon watan Yuli, Najeriya ta sake karyawa da labarin sace dalibai fiye da 100 na makarantar sakandare ta Bethel Baptist da ke karamar Chikun a Kaduna.
A farkon watan Nuwamba ne wasu 'yan bindiga su fiye da 50 suka girgiza birnin tarayya Abuja, bayan sun kutsa rukunin gidajen malaman jami'ar ta Abuja suka kwashi ma'aikatan jami'ar da 'ya'yansu su shida.
Mutuwar Shekau

Asalin hoton, AFP
Labarin da ya faranta ran hukumomi da 'yan Najeriya shi ne na kisan-kai da shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi inda rahotanni suka ce ya tashi bam din da ke jikinsa bayan da abokan adawa na bangaren ISWAP suka kutsa dajin Sambisa inda suka nemi tursasa masa yin mubaya'a.
A cikin wani sautin wata wanda kamfanonin dillancin labarai suka samu a watan Yuni, ƙungiyar ISWAP ta ce Shekau ya mutu ne a lokacin da ya kunna abin fashewa a jikinsa bayan karawa tsakanin ƙungiyoyin biyu.
A sautin, wanda ba a san lokacin da aka naɗe shi ba, wata murya da ake tunanin ta shugaban Iswap Abu Musab al-Barnawi ce, ta ce "ya kashe kansa nan take ta hanyar kunna abin fashewa".
Mayakan Iswap sun gano shugaban ƙungiyar Boko Haram ɗin ne kuma suka ba shi damar tuba ya koma cikinsu, a cewar al-Barnawi.
"Shekau ya gwammaci ya tozarta a lahira da ya tozarta a duniya," a cewarsa.
A ranar 25 ga watan Afrilun ne kuma wasu 'yan kungiyar Boko Haram sanye da kakin soji suka yi wa sojojin Najeriya kwantan-bauna, a garin Mainok mai nisan kilomita 36 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno, inda suka kashe soji 33.
Kifewar kwale-kwale a Kebbi da Kano

Wani labarin marar dadi da ya faru a watan Mayun 2021, shi ne na yadda wani kwale-kwale dauke da fasinjoji fiye da 150 a jihar Kebbi ya nutse, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum kusan 150.
Mutanen dai 'yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta dawowa daga cin kasuwa a makwabciyar jihar Neja.
A watan Nuwamba ne kuma wani kwale-kwalen fasinja a karamar hukumar Bagwai da ke jihar Kano, ya nutse da fasinjoji, inda kusan 30 suka mutu ciki har da kananan yara 'yan makarantar Islamiyya.
Rufe Twitter
A farkon Yuni ne kafar sada zumunta ta Twitter ta hadu da fishin gwamnatin Najeriya, bayan da kamfanin ya goge wani sako cikin jerin sakwannin da shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a a shafinsa inda yake gargaɗin 'yan awaren IPOB.
Kuma har kawo yanzu gwamnatin ba ta bude shafin ba, wani abu da ke sa ƴan kasar da suka damu da shafin yin zagaye domin amfani da shi.
Kama jagoran IPOB Nnamdi Kanu

Asalin hoton, Other
Shugaban kungiyar IPOB da ke son ɓallewa daga Najeriya, Nnamdi Kanu ya zo hannun hukumon Najeriya a karshen watan Yuni duk da cewa gwamnatin Najeriya ba ta fadi ƙasar da aka cafke shi ba.
An gurfanar da shi a gaban kotu kuma hukumomin Najeriya na ci gaba da tsare shi.
Kanu yana fuskantar zarge-zargen da suka shafi cin amanar kasa lamarin da ya sa aka gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa fafutukar da yake yi wajen ganin an kafa kasar Biafra ta hanyar IPOB.
Ana zarginsa da "hada kungiyoyi na tayar da zaune-tsaye, yada labaran karya, mallakar makamai ba bisa ka'ida ba da kuma shigowa da haramtattun kaya Najeriya."
Wanke Sheikh Ibrahim El Zakzaky

Asalin hoton, Other
A ƙarshen watan na Yuli ne wata babbar kotu da ke zama a Kaduna ta wanke shugaban kungiyar 'yan uwa Musulmi ta IMN, Sheikh Ibrahim Elzakzaky da mai dakinsa daga laifukan da ake tuhumarsu.
Babbar Kotun Jihar Kaduna ta bayar da umarnin a saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da matarsa Zeenat, inda ta wanke su daga dukkan zargin da ake yi musu.
A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke su daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar.
Hakan ne ya kawo ƙarshen zaman mutanen biyu a tsare har na kusan shekaru shida.
Hare-haren 'kuskure'

Asalin hoton, NIGERIAN AIRFORCE
A watan Satumba, wani jirgin sojin saman Najeriya ya yi luguden wuta a ƙauyen Kwatar Dabar Masara da ke jihar Borno, da manufar far wa 'yan kungiyar ISWAP, amma aka samu akasi inda aka kashe fararen hula tsakanin 50 zuwa 60.
An kuma samu irin wannan akasi a jihar Yobe mai makwabtaka inda wani jirgin yakin sojin saman Najeriya ya yi aman wuta a yankin kauyen Buhari da ke karamar Yunusari, inda ya yi sanadin mutuwar fararen hula guda 9.
Da farko rundunar sojin saman Najeriyar ta karyata rahoton BBC amma kuma daga baya sai ta yi amai ta lashe kayanta, inda ta ce an yi hakan amma bisa kuskure ne.
Hare-haren ƴan bindiga
A watan Oktoba ne kuma wasu 'yan bindiga suka bude wuta irin ta mai kan uwa da wabi a kan masallata yayin da suke sallar Asubahi, a garin Mazakuka da ke jihar Naija kuma nan take mutum 17 ciki har da limamin suka rasu.
A watan ne wasu da ba a iya tantance ko suwa ne ba suka dasa bam a layin dogo da ke tsakanin Abuja zuwa Kaduna, wani al'amari da ya janyo dakatar da zirga-zirgar jiragen na 'yan kwanaki.
Wannan al''amari ya tayar da hankalin fasinjojin da suka kauracewa bin hanyar mota daga Abuja zuwa Kaduna.
A watan Nuwamba, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa mayaƙan ISWAP da ke iƙirarin jihadi a yammacin Afrika sun halaka Birgediya Janar Dzarma Zirkushu da wasu sojoji uku, a lokacin da suka je kai ɗauki yayin wata ba-ta-kashi da mayaƙan.
A watan Disamba ne gungun matasa a arewacin Najeriya a jihohi daban-daban suka gudanar da zanga-zangar kiraye-kiraye ga gwamnatin Najeriya ta dauki matakin kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar yankin. Hakan dai ya bito bayan sanarwar da rundunar 'yan sandan jihar Sokoto da ke arewacin Najeriyar ta bayar cewa akalla mutum 21 ne wasu 'yan bindiga suka kona a wata motar fasinja lokacin da suka yi musu kwanton-bauna.
To sai dai wasu malamai irin su Sheikh Bala Lau sun ce addu'a ce mafita ba zanga-zanga.
Za a iya cewa shekarar 2021 ta zamo mai kalubale ga Najeriya musamman a sha'anin tsaro.











