Sarkin Abomey na Jamhuriyar Benin ya mutu

An yi wa Kêfa Sagbadjou Glèlè gani na ƙarshe a bainar jama'a lokacin da Faransa wadda a baya ta yi mulkin mallaka a kasar ta mayar da wasu dukiyar sarauta da aka sace.

Wani jami'in fada a Benin ya sanar da mutuwar Sarkin Abomey, Kêfa Sagbadjou Glèlè.

Sarakunan da suka gabace shi sun mulki Masarautar Dahomey, ɗaya daga cikin masarautu mafi ƙarfi a Afirka ta Yamma kafin zamanin mulkin mallaka.

An ba da rahoton cewa basaraken ya kai kimanin shekara 90, ko da yake ba a tabbatar da haƙiƙanin shekarunsa ba.

An yi masa ganin karshe a bainar jama'a a watan Nuwamba a wani buki na mayar da kadarorin sarauta guda 26 da Faransa ta marya wadanda sojojinta suka sace a karni na 19 .

Sun hada da mutum-mutumi, kofofin fada na ado da karagai biyu na sarauta.

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka fara yada rahotannin mutuwar sarkin, amma an tabbatar da labarin a ranar Alhamis, in ji kamfanin dillancin labarai na AFP.

"Masarautar ta afka cikin makoki. Sarki ya koma Sarki ya koma ga mahalacinsa a ranar Juma'a 17 ga watan Disemba," in ji Dako Kpogbemambou Vovoweyenonsin, wani babban jami'i a masarautar.

" Mun je masauratar da safe inda aka sanar da wannan labari mara dadi. Mutuwar sarkin ta tayar man da hankali ."

Marigayi Sagbadjou Glèlè ya hau kan karagar mulki ne a watan Janairun 2019, watanni shida bayan rasuwar magabacinsa Dadah Dedjalagni Agoli-Agbo, wanda ya shafe shekaru 30 yana mulki.

An kafa daular Dahomey ne, wanda Abomey ta kasance wani muhimmin bangarenta ne, a cikin shekarar 1600s. Amma a shekarar 1904 aka shigar da yankinsa karkashin mulkin mallakar Faransa kuma yanzu haɗeta a cikin kasar Benin .

Ta ci manyan birane da yaki a gabar tekun Atlantika tare da sayar da bayi ga turawa 'yan kasuwa da suka fito daga Turai inda suke bata bindigogi, arburussai da barasa.

An ba mata manyan mukamai a cikin masarautar har ma akwai rundunar zaratan sojoji wadda ilahirin dakarunta mata ne da ake kira Dahomey Amazons.